🏥 Magunguna

Kana cikin jima’i kawai sai Azzakarin ka ya kwanta yaki tashi

Kana cikin jima’i kawai sai Azzakarin ka ya kwanta yaki tashi

Kana cikin jima’i kawai sai Azzakarin ka ya kwanta yaki tashi

Ka taba shirin kwanciya da matarka amma dakazo sai gabanka yaki mikewa. Ko ka taba samun matsalar da gabanka yaki mikewa bayan zuwanka na farko kamar yadda ka saba.

Ko kasan abunda yake saka rashin yin sha’awar matarka akaiakai?

 

Wadannan tambayoyin ne zamu amsasu a cikin wannan darasin.

Akwai abubuwan dake haifarwa maza irin wadannan matsalolin kamar haka:

 

 

1: Tsabar Gajiya: Gajiya na cirewa namiji sha’awar Jima’i. Yakan sa gaban namiji yayi rauni. Haka nan yakan jawo saurin zuwan kai.

 

Kada namiji yace zai tilasta kansa yin Jima’i bayan yasan yana gajiye. Haka nan mata kada tace tunda tana cikin sha’awa dole mijinta ya sadu da ita bayan ya gaji.

 

Duk cikinsu biyu wanda yayi hakan sai ya gwammace da ma bai soma ba. Domin cikin abubuwan nan da muka ambata guda ko dukkaninsu suna iya faruwa.

 

Sai dai akwai wasu mazan da sha’awar su na jima’i na motsawa ne a lokacinda suke gajiye.

 

2: Matsalar Rayuwa: Duk namijin dake cikin matsala irin na rayuwa bai iya gamsar da matarsa yadda ya kamata.

Jima’i akan yishi ne da kwakwaluwa amma bada gangan jiki ba. Muddin kwakwaluwar mutum bata natsai, bazai ma ji sha’awa ba bare har ya iya gamsar da matarsa. Amma su mata, saduwa dasu yakan gusar musu da matsalar rayuwa da suke ciki. Shi yasa zaka ga kana cikin tunanin kudin cefenan da zakuci abinci gobe, kudin hayar gida, kudin makarantan yara, ita kuwa matarka tana kaiwa gabanka cafka domin motsaka. A hakan koka motsu sai ka kasa yin wani katabus ita kuwa ta soma gungunin ba a gamsar da ita ba.

 

3: Yawan Kallon Batsa: Idan namiji ya saba da kallon fina finai na batsa zai rika kasancewa bai da sha’awa har sai idan ya kalli wadannan shirin kamin ya motsu.

 

Duk irin kusanci da mace zata yi dashi, duk wasan da zata masa hankalinsa fa bazai motsa sha’awar sa ba sai kodai ya kawo wani fim a ransa ko kuma ya kunna kallon kamin nan ya iya gamsar da matarsa.

Wannan yana daya daga cikin illar sabo da kalon fim na batsa kenan.

4: Sabo Da Shan Kwayoyin Jima’i: Idan namiji ya saba duk saduwa da matarsa sai ya sha wani abunda zai kara masa sha’awa ko kuzari, bazai iya gamsar da matarsa ba a lokacinda bai samun wannan abun ba.

 

Ba lalle bane sai kwaya ba, akwai mazan da muddin basu sha giya ko sun zuki tabar wiwi ba basu da sha’awa ko kuzari cin matansu.

 

5: Baida Bukata: Rashin bukatar namiji ya sadu da matarsa shima yakan jawo raunin gaban namiji.

Zaki ga kinyi masa wasa gabansa ya Mike amma kuma sai nan da nan ya sake kwanciya. Hakan yake muddin dai ba namiji yana tsaka da bukatarki bane.

 

Wannan yasa yake da kyau ma’aurata ya zamto sunada wata inkiyar da suke yiwa juna na bukatar Jima’i tun kamin ma namiji ya shigo gida bayan fitarsa nema.

 

Idan mace ke da bukatar mijinta tayi amfani da darusan da muka koyar na yadda ake motsawa namiji sha’awa kamin ma ya dawo gida. Haka nan idan shi mijin ke bukata. Hakan zai taimakawa ma’auratan su kimtsa domin samun damar gamsar da junansu.

 

Allah yasa mu dace ameen summa ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button