📻 Labaran Hausa

Abba Gida-Gida Zai Yiwa Murja Kunya Sakayya, Zai Yi Mata Aure Daga Cikin Zaurawan da Zai Aurar

Abba Gida-Gida Zai Yiwa Murja Kunya Sakayya, Zai Yi Mata Aure Daga Cikin Zaurawan da Zai Aurar

Abba Gida-Gida Zai Yiwa Murja Kunya Sakayya, Zai Yi Mata Aure Daga Cikin Zaurawan da Zai Aurar

Ayyiriri : Abba Gida Gida zai aurar da murja kunya

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar cewa zai aurar da fitacciyar jarumar nan ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.jaridar aminiya na ruwaito wannan rahoto.

Abba Gida-Gida wanda ya sanar da hakan a Fadar Gwamnatin Kano ya ce zai aurar da jarumar ce a cikin zawarawan da gwamnatinsa ke shirin aurarwa kwanan nan.

Gwamnan ya ce zai yi wa Murja wannan tagomashi ne la’akari da gudunmawar da ta rika bai wa gwamnatinsa tun gabanin ya lashe zaben da aka yi a watan Maris, har zuwa yanzu.

A cewarsa, “kowa ya san irin rawar da Murja ta taka wajen yayata ayyukan alheri da gwamnatin nan ke yi, wanda babu abin da za mu ce sai son barka.

Kuma ita ce ta fara fitowa a cikin ’yan group dinsu [’yan TikTok] ta ce tana son a yi mata aure sunnar Manzon Allah.

“Matar da ta fito ta ce tana son a inganta sunna ta Manzon Allah ai ba a bar kyama ce.

“Kuma so take ta je inda za ta ba da gudunmawar inganta addinin Musulunci.”

Gwamnan jihar Kano ya bayyana aniyarsa na aurar da Murja Kunya a shirin auren zaurawa da gwamnatinsa ta tsara a jihar.

A cewarsa, ta yi kokari wajen tabbatar da gwamnatinsa ta kafu, don haka za a yi mata sakayya da alherin aure sunnar ma’aiki.

Gwamnatin Kano ta ware kudade da dama domin yiwa zaurawa aure a jihar, inda tuni aka fara shirin yadda hakan za ta kasance.

Jihar Kano – Fitacciyar ‘yar TikTok, Murja Kunya za ta amarce a auren zaurawa da za a gudanar nan ba da jimawa ba a jihar Kano.

Wannan na fitowa ne daga bakin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida yayin da yake jawabi, Aminiya ta ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button