Wata Mata Ta Haifi Yara 9 Cikin Shekaru 13, Ta Ce Saura Na Nan Tafe
Tun bayan da Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong suka yi aure, suna haihuwar sabon ‘da duk shekara.
Sun yi sauki ne a 2020 lokacin da annoba ta barke kafin suka koma bakin aiki bayan abubuwa sun koma daidai.
Masoyan wadanda ke ganiyar shekaru 30 da doriya suna da yara tara a yanzu haka, suna tsammanin haihuwar na 10 kuma basu shirya dakatawa nan kusa ba.
Wata yar kasar China mai suna Tian Dongxia da mijinta Zhao Wanlong sun ja hankalin jama’a bayan sun haifi yara tara a cikin shekaru 13 da suka gabata.
A cewar Mothership, matar wacce ke ganiyar shekaru 30 da doriya ta haifi diyarta ta farko a 2010.
Sufara soyyaya a makaranta.
Da aka tambayeta kan dalilin da yasa take haihuwa ba kakkautawa, ta bayyana cewa bata so ta “yi asarar kwayoyin halittar mijinta.”
Ta ci gaba da bayanin cewa hikimarta shine ci gaba da haihuwar yara har sai ta kai 12 don kowani yaro ya wakilci ‘ilimin taurari’ na kasar China.
“Na fada tarkon son Tian a ganin farko da nayi mata lokacin muna babbar makaransa sannan na fara bibiyarta har sai da ta yarda ta so ni,” Zhao ya bayyana.
A 2012, shekaru biyu bayan Tian ta haifi diyarsu ta farko, sai Allah ya azurta ma’auratan da haihuwar yan biyu maza.
Sunyi sauki saboda annoba.
Bayan su haifi yara uku, Tian da Zhao sun ga cewa lokaci ya yi da za su dakata, amma Tian tace ta ji tana son haihuwar karin yara domin gidan ya zama cikin walwala.