📻 Labaran Hausa

Innalillahi Wa’inna Illahi Raji’un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa

Innalillahi Wa'inna Illahi Raji'un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa

Innalillahi Wa’inna Illahi Raji’un: Allah Ya Yi Wa Jarumar Kannywood Hannatu Umar Rasuwa

Fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Hannatu Umar ta kwanta dama.

Hannatu ta rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta, kuma tuni aka sada ta da gidanta na gaskiya.

Shugaban kungiyar tace fina-finai na jihar Kannywood, Abba Al-Mustapha ya mika ta’aziyyarsa kan rasuwar abokiyar sana’ar tasa.

Labari da ke zuwa mana a yanzu shine cewa Allah ya yi wa shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Hannatu Umar rasuwa.

Shugaban kungiyar tace fina-finai na jihar Kannywood kuma babban jarumi, Abba Al-Mustapha ne ya sanar da labarin mutuwar jarumar a shafinsa na Instagram.

Jarumar wacce ta yi suna a fim dinta na ‘Jarumai’ ta rasu ne a ranar Lahadi, 20 ga watan Agusta, kuma tuni aka yi jana’izarta daidai da koyarwar addinin Musulunci.

Ga yadda ya wallafa a shafin nasa:

“INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJIUN

“Allah yayi wa Jaruma HANNATU UMAR(JARUMAI) rasuwa kuma tuni anyi jana’izarta Kamar yadda Addinin musulunci ya tanadar.

“Muna Addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata kurakuranta yasa Aljanna ce makomarta. Idan tamu tazo Allah yasa mu cika da kyau da Imani.

“R.I.J.F ”

Jama’a sun nuna alhini a kan rasuwar Jaruma Hannatu

Allah ya jikanta da rahama 🙏🙏.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button