📻 Labaran Hausa

Yadda yunwa tayi sanadiyar mutuwar wata budurwa a arewacin najeriya

Yadda yunwa tayi sanadiyar mutuwar wata budurwa a arewacin najeriya

Yadda yunwa tayi sanadiyar mutuwar wata budurwa a arewacin najeriya

Innnah lillahi wah innah ‘ilaihi raji’un.Wata budurwa ta rasu a unguwar cikin wani gari, bayan an binneta sai mahaifinta ya mike tsaye a gaban mutane yana kuka.

Budar bakinsa sai akaji yana fadin jama’a wallahi yunwa ce ta kashe yarinyar nan sakamakon kuncin rayuwa da muka sami kanmu a ciki.

Yace a yanzu haka yau kwanan mu kusan sama da arba’in iya sau daya muke samun damar cin abinci a kullum.

Ya ‘kara da cewa cin abinci sau daya a ranarma wataran baya isar mu, idan kuma mun nemi taimakon agun jama’a mai kokarin da zai taimake mu baya wuce ya bamu naira 500 ko 1000 ga tarin iyali.

Da taga haka sai ta ‘kudiri aniyar kama azumi kusan kullum tana cikin azumin, cikin wannan yanayin har ulcer ta kamata saboda idan tazo bude baki (iftar) abin da zata cin baya isarta, haka sahur dinma maleji take yi.

A ‘karshe dai yau gashi ta koma ga mahaliccinta sakamakon yunwa da jinyar ulcer data kamata har kwananta ya kare.

Yana da kyau al’ummah masu dama-dama suna kokarin taimako a wannan yanayin da ake ciki, mutane suna cikin kunci ga kuma wasu da iyalai masu yawa.

Wallahi da naji wannan labarin bansan lokacin da hawaye suka zubo min a idanuwana ba saboda tausayi.

Mun yi copied na wannan labari ne, mun kuma masa gyara na rubutun domin masu dan dama-dama su farga wajan taimakon marasa hali.

Allah ya bawa masu dama taimakon marasa karfi, ya kawo mana karshan wannan masifa da muka samu kanmu a ciki.

Ameeeen Yah Hayyuh Yah Qayyum

Allah yasa mudace ameee summa ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button