yadda amarya ta gano angonta yayi zina da wata a ranar daurin aurensu
A yau mun sake zo muku da wani labari mai ban al’ajabi da mamaki irin yadda amarya ta fahimci cewa ranar da take zumudin haduwa da sahibinta amma sai da ya nemi wata yayi lalata da ita jaridar Leadership hausa sun ruwaito labarin a cikin wani shiri nasu mai duna taskira ga yadda labarin ya kasance.
Jama’a barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki har da abin da ya shafi zamantakewar aure. Kamar sauran makonnin da suka gabata, shafin Taskira ya karbi sakonni daga wajen mabiya shafin, wanda a yau ma shafin ya ci karo da wani sakon, inda aka bukaci boye sunan wadda ta aiko da shi, sakon ya fara da cewa:
“Assalamu Alaikum dan Allah ina so a ba ni shawara, ina cikin tashin hankali, ji nake kamar na kashe kaina. Yau sati na uku da yin aure, amma na ji duk duniya da ban yi auren ba. Wallahi mijina mazinaci ne, yau kwana 4 kenan da na ga abun da idona, wallahi tun ranar da na gani wani jiri ya dauken har yau ba ni da lafiya.
Mijina ya fita sallar Asuba sai wuta ta dauke na dauki wayarshi na kunna haske, ina zaune ina Tasbihi kamar da wasa na shiga ‘Gallery’ din wayarsa wallahi hotunan banza da bidiyon iskanci duk a wayar, sai na ga ta WhatsApp aka turo mishi, shi ne na shiga WhatsApp din wallahi ‘yan matan da ya ke ‘charting’ din banza da su sun fi goma. Wallahi a yadda na fahimci chat dinsu da wata a ranar aurenmu sai da ya yi zina, har tana ce mishi ya tafi daurin aurensa ya bar ta cikin ‘sparm’ din shi, wallahi har labarin ‘first night’ dinmu ya bawa wata, wai “salam ya jini?”, wai dan Allah ta shirya tarba gobe zai zo kuma sai da ya je din.
Wallahi da na tuna ‘Date’ din tun safe ya fita ya ce mun zai je banki bai dawo ba sai bayan Azahar ashe zina ya je ya yi, wallahi a yadda na fahimta wallahi ba karamin mazinaci ba ne. Ni dai yanzu shawarar da za ku ba ni yadda zan nemi saki ne, saboda wallahi gara na kare rayuwata ba aure da na zauna da wannan mutumin, kuma dukka bai wuce shekara 30 ba, amma ya gama lalata rayuwarshi, kuma ku taya ni rokon Allah ya sa ban dauki cikinsa ba”.