📻 Labaran Hausa

ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWA SAMA DA 20 SUN AIKEWA SHUGABAN ƘASA TINUBU SAƘON GODIYA BISA NAƊA MARYAM SHETTY MUƘAMIN MINISTA

ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWA SAMA DA 20 SUN AIKEWA SHUGABAN ƘASA TINUBU SAƘON GODIYA BISA NAƊA MARYAM SHETTY MUƘAMIN MINISTA

ƘUNGIYOYIN MATASAN AREWA SAMA DA 20 SUN AIKEWA SHUGABAN ƘASA TINUBU SAƘON GODIYA BISA NAƊA MARYAM SHETTY MUƘAMIN MINISTA

 

-Ƙungiyoyin Sun Jinjinawa Shugaban Ƙasa Kan Ƙoƙarinsa Na Ya Zaɓo Mace Matashiya Ƴar Arewa Ya Ba Ta Wannan Matsayi Na Minister

 

-“Mai Girma Shugaban Ƙasa Tunda Har Ka Zaɓi Hajiya Maryam Shetty Cikin Ministocinka To Mu Na Ba Ka Tabbacin 2027 Ba Ka Da Matsala, Ka Shiga Ɗaki Ka Yi Bacci Ka Ci Zaɓe A Arewa Domin Ita Kaɗai Gayya Ce”. Cewar wasiƙar.

 

A wani lamari da ke nuna yadda Hajiya Maryam Shetty ke da kykkyawar alaƙa da matasan Arewa ba iya na Jihar Kano kaɗai ba, sama da ƙungiyoyin matasa guda 20 sun aikewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wasiƙar yabo da godiya bisa zaɓo Hajiya Maryam Shetty da ya yi daga cikinsu ya ba ta muƙamin minista.

 

Ƙungiyoyin sun bayyana cewa wannan ƙoƙari ne abin yabo da jinjina wanda shugaban ƙasar ya yi da ba a taɓa samun kamarsa ba a tarihin Nageria.

“Ya mai girma shugaban ƙasa, haƙiƙa mu na matuƙar godiya da jinjinar ban girma a gare ka bisa wannan ƙoƙari naka na zaɓo ƴar uwarmu matashiya ka ba ta muƙamin minista, wannan abu ne da mu ka jima mu na fatan gani a ƙasar nan ba mu samu ba sai kai ne ka ba mu wannan dama ta damawa da mata matasa”. Cewar wasiƙar ƙungiyoyin.

Daga nan wasiƙar ta cigaba da cewa “Mai girma shugaban ƙasa, wannan mataki da ka ɗauka na damawa da mata matasa cikin gwamnati, mataki ne da duk ƙasashen duniya waɗanda su ka cigaba su na aiwatar da shi, Nageriya aka bari a baya sai yanzu da ka zo ka ɗauki matakin aiwatarwa ka zaɓo mata matasa daga Arewaci da Kudancin ƙasar nan ka naɗa su ministoci wanda hakan ba ƙaramar nasara ce da cigaba a gwamnatinka ba. Haƙiƙa tarihi ba zai taɓa mantawa da kai ba, mun yaba maka”. Su ka ce.

Daga ƙarshe kuma wasiƙar ta ƙarƙare da cewa “mai girma shugaban ƙasa, Hajiya Maryam Shetty matashiyar ce jajirtacciya, haziƙa mai juriya da himma. Mun san irin ƙoƙari da gudunmawar da ta bayar wajen samun nasararka a 2023, mun tabbata wannan muƙami na minista da ka ba ta a yanzu zai ƙara mata ƙaimi da ƙarfin gwiwa ne wajen ninka ƙoƙarinta a shekarar zaɓe ta 2027. Mai girma shugaban ƙasa tunda har ka zaɓi Maryam Shetty cikin ministoci to mu na ba ka tabbacin 2027 ba ka da matsala, ka shiga ɗaki kayi bacci ka ci zaɓe a Arewa domin ita kaɗai gayya ce”. Cewar wasiƙar.

A wata mai kama da wannan, wani malamin addinin musulunci daga Jihr Kanø, Shaikh Abu Ammar, ya yi kira ga matasan Arewa su yi koyi da kyawawan halaye da ɗabi’un Maryam Shetty domin su ma su zama abin alfahari cikin al’umma. “Ba shakka kyawawan halaye da ɗabi’u gami da juriya da himmar Dr. Maryam Shatty su ne silar samar mata wannan muƙami na minista, akwai buƙatar sauran matasanmu na Arewa su yi koyi da ita ko sa samu nasarar zama kamarta”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button