Manyan Dalilan Dasuka Kawo Juyin Mulki A Niger Yanzu Bidiyo Ta Ɓulla
Ga video nan kasa 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Wani yuƙurin juyin mulki da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar, ya fuskanci Allah-wadai daga ɓangarori daban-daban na duniya ciki har da Tarayyar Afirka da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Amurka.
Tun da sanyin safiyar Laraba ne dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa suke tsare da Shugaba Mohamed Bazoum a fadarsa da ke babban birnin Niamey.
Wata sanarwa daga fadar shugaban Nijar ta ce sojojin ƙasar za su kai hari a kan dakarun tsaron fadar Bazoum matuƙar ba su janye ba.
Rundunar sojojin ƙasar ga alama tana ci gaba da yin biyayya ga shugaban ƙasar kuma ba za a samu rahotannin ɓarkewar harbe-harben bindiga
Kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar har yanzu tana ci gaba da yaɗa shirye-shirye; sai dai ba ta ambaci aukuwar wani yamutsi ba.
Dakarun tsaro na musamman masu biyayya ga Shugaba Bazoum sun ja daga a zagayen gidan talbijin ɗin ƙasar da kuma fadar shugaban na Nijar.
Tarayyar Turai ta bayyana matakin sojojin a matsayin cin amanar ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce lamarin shi ne juyin mulki ko yunƙurin juyin mulki na tara cikin shekara uku kawai a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, yankin da a shekara goma ya yi namijin ƙoƙari don watsar da laƙabin da ake masa na “sashen juyin mulki”, kafin taɓarɓarewar tsaro babu ƙaƙƙautawa da cin hanci su sake buɗe ƙofa ga sojoji.
A shekarun baya-bayan nan an samu juyin mulki a Mali da Burkina Faso. Duka maƙwabtan na Nijar sun ba da umarni sojojin Faransa su fice daga cikin ƙasashensu kuma sun ƙulla ƙawance da Rasha.
Nijar, babbar abokiyar ƙawance ce ga Ƙasashen Yamma masu dama ciki har da Faransa da Amurka a yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Afirka ta Yamma.
Nijar ta yi fama da juyin mulkin sojoji har sau huɗu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960.
Masu shiga tsakani daga Ecowas sun isa Niamey
Shugaban ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu ya ce takwaransa na Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya kai ziyara birnin Niamey a wani yunƙuri don shiga tsakani game da yunƙurin juyin mulki a Nijar.
Wani jirgin saman shugaban Najeriya ya sauka a Niamey kuma ga alama yana ɗauke da masu shiga tsakanin na ƙungiyar Ecowas, cewar rahotanni.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato Shugaba Tinubu yana cewa Patrice Talon yana kan hanyar zuwa can yanzu don ƙoƙarin shiga tsakani.
Talon ya nufi Nijar bayan wata ganawa da Bola Tinubu a birnin Abuja.
Ba za mu yarda da juyin mulki ba – Tinubu
Skip podcast promotion and continue reading

Korona: Ina Mafita?
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Kashi-kashi
End of podcast promotion
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunƙurin juyin mulki a Jamhuariyar Nijar.
Shugaban ƙungiyar kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ne ya bayyana wannan matsayi bayan rahotanni a safiyar Laraba sun ce dakarun tsaro sun toshe fadar shugaban ƙasa da ofisoshin jami’an gwamnati a ƙasar.
A martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa, Tinubu ya ce ba za su lamunci yunƙurin juyin mulkin sojoji ba.
Ecowas cikin kakkausan murya ta ce ta yi Allah-wadai da abin da ta kira duk wani yunƙurin ƙwace iko da ƙarfi kuma “muna kira ga masu shirya juyin mulkin su saki zaɓaɓɓen shugaban dimokraɗiyya nan take ba tare da wani sharaɗi ba”.
Ta ce ƙungiyar da al’ummar duniya za su riƙe duk waɗanda ke hannu a wannan yunƙuri da alhakin tsaro da kare lafiyar shugaban ƙasa da iyalinsa da kuma jami’an gwamnati da sauran al’ummar Nijar.
Shi dai Shugaba Tinubu ya ci gaba da cewa “Kamata ya yi duk ‘yan Jamhuriyar Nijar su fahimci cewa shugabancin ECOWAS da duk masu ƙaunar dimokradiyya, ba za su amince da duk wani yanayi da zai kawo cikas ga gwamnatin da aka zaɓa bisa tsarin dimokraɗiyya a ƙasar ba.”
“Shugabancin ECOWAS ba zai amince da duk wani mataki da zai kawo cikas wajen gudanar da halastacciyar gwamnati a Nijar ko wani yanki na Afirka ta Yamma ba.”
“Ina son na ƙara da cewa muna sa ido sosai kan al’amura da abubuwan da ke faruwa a Nijar kuma za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da ganin dimokraɗiyya ta ci gaba da kafuwa da bunkasa a kan ingantaccen tushe a yankinmu.”
“Ina tuntuɓar sauran shugabanni a yankinmu, kuma za mu kare dimokraɗiyyar da muke taƙama da ita bisa tsarin mulkin ƙasa wanda kowa ya yarda da shi.”
Tinubu ya ƙara da cewa, a matsayinsa na jagora a ƙungiyar ECOWAS, Najeriya za ta tsaya tsayin daka tare da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Nijar, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen karewa da kiyaye tsarin mulkin kasar.
AU ta yi tur da ‘cin amanar mulkin jamhuriyya’
Ita ma, Tarayyar Turai ta bayyana cewa “ta damu matuƙa kan abubuwan da ke faruwa a Nijar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato babban jami’in kula da manufofin hulɗa da ƙasashen wajen ƙungiyar Josep Borell a ranar Laraba yana bayyana haka bayan rahotannin wani yunƙurin juyin mulki.
Ya ce Tarayyar Turai ta yi Allah-wadai da duk wani yunƙuri na wargaza tsarin dimokraɗiyya da kuma barazana ga kwanciyar hankali a Nijar.
Tarayyar Afirka ma ta yi Allah-wadai da ‘yunƙurin juyin mulki a Nijar’.
Wata sanarwa da shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Paki Mahamat ya fitar ta ambato shi yana cewa an sanar da shi game da yunƙurin wasu jami’an sojoji na yin zagon ƙasa ga kwanciyar hankalin dimokraɗiyya da cibiyoyin kare jamhuriyya a Nijar, a wani abu mai kama da yunƙurin juyin mulki.
Ƙungiyar ƙasashen Afirkan dai ta yi tur da matakan da sojojin suka ɗauka wanda AU ta ce tamkar cin amanar nauyin da aka ɗora musu ne na kare mulkin jamhuriyya. Ya yi kira ga sojojin su dakatar da matakan da ya ce ba za a yarda da su ba.
Shugaban Hukumar AU ya kuma yi kira ga al’ummar Nijar da dukkan ‘yan’uwansu na Afirka musamman ƙasashen ECOWAS da ma na faɗin duniya, su buɗe muryoyinsu wajen yin Allah-wadai gaba ɗaya da wannan yunƙurin juyin mulki.
Dakaru sun toshe fadar Shugaba Bazoum
Tun farko, dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ne suka toshe duk wata hanyar zuwa fadar.
Sai dai rahotanni na cewa yanzu haka wasu tsofaffin shugabannin Nijar na tattaunawa da sojojin a ƙoƙarin sasanta al’amarin.
Jamhuriyar Nijar na cikin ƙasashen Afirka da suka fi fama da juyin mulki bayan samun ƴanci daga Turawan Mulkin Mallaka a 1960.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar masu tsaron fadar shugaban sun toshe duk wata hanyar zuwa gidan shugaban ƙasa a birnin Yamai, amma babu wani rahoto na harbin bindiga.
A shekara ta 2021 ne aka zaɓi Bazoum a matsayin shugaban ƙasar ta Nijar.
Bazoum Mohammed na cikin shugabannin Afirka da aka yi amannar suna ɗasawa da ƙasar Faransa, wadda ta yi wa Nijar jmulkin mallaka.
Juyin mulki na ƙarshe da aka yi a jamhuriyar Nijar ya faru ne a 2010, lokacin da aka tuntsirar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Tandja Mamadou.
Haka kuma, ƙasar na fama da rikicin masu iƙirarin jihadi waɗanda ke tayar da ƙayar baya, lamarin da ya yi ƙamari a wasu ƙasashen Afirka ta Yamma da dama, kamar Mali.
Abin da muka sani zuwa yanzu
Dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa tun farko sun toshe hanyar zuwa fadar shugaban Nijar
Ana shiga halin ruɗani da zaman rashin tabbas a Niamey.
Rahotanni sun ce ana tsare da Shugaba Mohammed Bazoum a wani abu mai kama da juyin mulki
Fadar shugaban ƙasa ta ce duk wani yunƙurin kawo hargitsi, ba zai yi nasara ba
Ƙungiyar raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce ta damu game da wani yunƙurin juyin mulki a Nijar.
Majiyoyi sun ce ana tattaunawa da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasar inda tsohon shugaban Nijar Mouhammadou Issoufou da tsohon babban hafsan sojojin ƙasar Salifou Moudi suke shiga tsakani.
Nijar ta shaida juyin mulki har karo huɗu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960.
Ba a samu rahotannin jin ƙarar harbe-harbe ba yayin da ‘yan ƙasar ke dakon su ji abin da taƙamaimai yake faruwa.
Sojojin ƙasar sun yi barazanar kai hari kan dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa, matuƙar suka ƙi janyewa.
Masu nazari na cewa abin da ke faruwa ya nuna tamkar dakarun tsaron fadar shugaban ƙasar ba su samu haɗin kan sauran rundunonin sojoji ba.
Ga ƙarin hotunan yadda wasu titunan birnin Yamai suka kasance ranar Laraba
Da yammacin Laraba, an ga wasu masu zanga-zangar nuna goyon bayan Shugaba Bazoum sun taru a gaban ginin Majalisar Dokokin Nijar.
Masu zanga-zangar akasarinsu ‘ya’yan jam’iyyar PNDS Tarayya na kiran a kawo ƙarshen yunƙurin juyin mulkin.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun nufi hanyar fadar shugaban ƙasa, kafin a tarwatsa su gabanin su isa inda suka yi niyya.
Amurka ta nemi a saki Bazoum
Amurka ta bayyana tsananin damuwa kan abubuwan da ke faruwa a Nijar.
Kuma cikin kakkausan harshe ta yi Allah-wadai da duk wani ƙoƙari na tsarewa ko yin zagon ƙasa ga zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokraɗiyya a ƙasar ta Afirka.
Mashawarcin Tsaron Ƙasa, Jake Sullivan ya faɗa a ranar Laraba cikin wata sanarwa cewa takanas muna kira ga jami’an tsaron fadar shugaban ƙasa su saki Bazoum Mohammed kuma su guji amfani da ƙarfi.
Sanarwar ta ƙara da cewa fadar White House na ci gaba da bibiyar al’amura a ƙasar don tabbatar da ganin Amurkawan da ke can suna cikin aminci.
Shi ma Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi tur da duk wani ƙoƙarin na ƙwace mulki ta ƙarfi da yaji a Nijar, kuma ya yi kira ga duk waɗanda lamarin ya shafa su kai zuciya nesa.
Wata sanarwa da ya fitar, ta ce babban sakataren yana bibiyar al’amuran da ke faruwa a Nijar.
Ita ma gwamnatin Faransa ta ce tana Allah-wadai da duk yunƙurin ƙwace mulki ta hanyar amfani da ƙarfi a Nijar.
Wata jami’a mai magana da yawun gwamnatin Faransa ta ce ƙasar ta bi sahun Tarayyar Afirka wajen yin kira a dawo da martabar tsarin dimokraɗiyya a Nijar.
Ta kuma shawarci Faransawan da ke zaune a babban birnin Nijar su sa ido.
AFP ya ruwaito cewa dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa ne suka tarwatsa masu zanga-zangar ta hanyar yin harbe-harben gargaɗi don wargaza taron masu macin.
Magoya bayan Shugaba Bazoum sun tunkari ginin fadar shugaban ƙasar ne, inda ake tsare da Bazoum, amma amon bindigogi ya sanya su ranta a cikin na kare.
Allah yasamudace Ameen summa Ameen 🤲 🤲.