🏥 Magunguna

SÒ GAMON JINI: “Daga Yau Na Shiga Cikin Manema Aurenki” Saƙon Matashin Ɗan Kasuwa Bilyameen Gunduwawa Ga Jarùmar Kannywood A’isha Humaira

SÒ GAMON JINI: “Daga Yau Na Shiga Cikin Manema Aurenki" Saƙon Matashin Ɗan Kasuwa Bilyameen Gunduwawa Ga Jarùmar Kannywood A'isha Humaira

SÒ GAMON JINI: “Daga Yau Na Shiga Cikin Manema Aurenki” Saƙon Matashin Ɗan Kasuwa Bilyameen Gunduwawa Ga Jarùmar Kannywood A’isha Humaira

“Ni Ɗan Kasuwa Ne, Sannan Kuma Ina Da Gida Da Abin Hawa, A Shirye Na Ke Tsaf! Na Auri A’isha Humaira Dazarar Ta Ba Ni Dama”. Cewar Bilyameen.

Wani Matashin ɗan kasuwa mai suna Bilyameen Gunduwawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Jihar Kano, ya bayyana tsananin ƙaunarsa ga fitacciyar Jaruma a masana’antar Kannywood, kana kuma ta hannun daman shahararren mawaƙin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara, wato A’isha Ahmad Idris, wacce aka fi sani da (A’isha Humaira).

“Daga yau na shiga cikin manema aurenki”. Wannan shi ne saƙon da matashin ya wallafa a (Comment Section), a ƙarƙashin wani Posting da A’isha Humairan ta yi a shafinta na Instgram, inda ta wallafa bidiyonta da sautin waƙar soyayya ta na rausayawa.

A tattaunwar da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta yi da Matashin ya bayyana cewa yanzu haka ya na da kimanin shekaru 31 a Duniya, sannan kuma ƙwayar halittarsa, wato (Genotype), ta na rukanin (AS).

Baya da haka kuma ya na harkokin kasuwanci, sannan kuma ya na aiki da wani kamfani mai zaman kansa. Daɗi da ƙari kuma ya na da kammalallen gida haɗi da abin hawa. Dan haka ya shirya tsaf! Ya auri A’isha Humaira dazarar ta ba shi dama.

Mè zakù cè?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button