Yadda mahaifiyar abba elmustapha da yan uwansa da iyalinsa suka ziyarci ofishinsa
Abba elmustapha ya shiga ofis a satin da ya gabata domin kama aiki gadan gadan na jagorancin da anka bashi.
Abba elmustapha ya samu bakwanci da ziyarar mahaifiyarsa da yan uwansa da iyalensa na kai masa har ofis dinsa.
Inda ya wallafa kamar haka.
“A L H A M D U L I L L A H
Mahaifiyata(Gwagwgo) da kuma ‘Yan Uwana tare da Iyalina sun kawo mun ziyarar taya ni murna hade da Fatan Alheri Alheri a Office dina.
S A I G O D I Y A
#abbanaabba2027″
Ga hotunan nan.
Ali Nuhu Da Bashir Maishadda sun goyi bayan Soke lasisin yan Kannywood
A jiya ne anka samu sanarwa saga shugaban hukumar tace fina finai a jihar Kano Abba elmustapha yace sun soke duk wani lasisi da yan Masana’atar Kannywood da kuma gidan gala.
Shugaban ya bayyana cewa saboda sun fahimci kowa jarumi mai daukar hoto ko bidiyo inda yace dole ne sai an tantance duk wani mai son zama jarumi.
Abba elmustapha yace sake da cewa yanzu suna son duk wanda zai samu lasisi sai sun aminta da nagartasa da ingancinsa kafin ya samu wannan lasisi.
Shine jarumi Ali Nuhu ya aminta da wannan kudirin abba elmustapha inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
“Muna goyon bayanka, Allah ya bada ikon sauke nauyin Mai girma ES @abbaelmustapha1”
Shima dai ga abinda bashir Maishadda ke cewa.
“Kannywood Babbar Masana’anta ce, kuma uwa ce maba da mama. GASKIYA ya kamata a tsaftace ta da bara gurbi.
Ni Mai Shirya Fim ne, kuma Mai Daukar Nauyi + Na Goyi bayan hakan Dari bisa dari.
Da fatan kowacce kungiya zata yi kokarin tantance mutanen ta.
Allah ya taimaki Kannywood
@abbaelmustapha1″