📻 Labaran Hausa

Rundunar yan sanda ta kama wata Amarya bisa zargin guntule mazaƙutar Angonta a karamar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina.

Rundunar yan sanda ta kama wata Amarya bisa zargin guntule mazaƙutar Angonta a karamar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina.

Rundunar yan sanda ta kama wata Amarya bisa zargin guntule mazaƙutar Angonta a karamar hukumar Ƙafur ta jihar Katsina.

 

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce a halin yanzu Angon na kwance a Asibitin Malumfashi.

 

Ya ce hukumar zata gurfanar da matar gaban Kotu da zaran ta karkare bincike kan abinda ya faru.

 

Katsina state – Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina, ta tabbatar da cafke wata amarya mai suna Tinene Isa, bisa zargin yanke mazaƙutar mijinta.

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Aliyu, ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ranar Laraba a Katsina.

 

ASP Aliyu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kafur da ke cikin jihar Katsina, Arewa maso Yammacin Najeriya, kamar yadda jaridar daily Nigerian ta ruwaito.

 

Kakakin yan sandan bai faɗi sunan Angon da wannan lamari ya faru da shi ba amma ya ce a halin yanzu yana kwance a babban Asibitin Malumfashi ana kulawa da shi.

 

Ya kuma yi bayanin cewa Amaryar da ake zargi da aikata wannan ɗanyen aiki, ta yi amfani da reza mai kaifi wajen gutsire wa Angonta mazaƙutarsa.

 

A kalamansa, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan Katsina ya ce:

 

“Na gaya muku, muna kan gudanar da bincike kan lamarin ne a halin yanzu. Amarya ce kuma ta haura shekara 30 a duniya.

 

“Watakila ta dauki lokaci mai tsawo kafin ta yi aure, ko kuma wannan ba shi ne aurenta na farko ba.”

 

“Ba ni da cikakken bayani, za mu gano duk wadannan da sauran bayanai a bincikenmu.”

 

A cewarsa, hukumar ‘yan sanda zata gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotu da zaran an kammala bincike kan ainihin abinda ya faru, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

 

A wani labarin na daban Wata mata ‘yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta duƙa kan guiwa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.

 

Ma’auratan sun sha dirama kan haka a wani gajeren bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

Allah ya sa mudace ya zabamu da aikin dana sani

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button