Idan har kin kai mace a fuska amma kuma kinaji a jikin ki tamkar baki kai ba to kiyi amfani da wannan hadin maganin
A cikin kaso saba’in na mata a wannan zamanin zaka gansu ne suna da cikar sura ta mata, ma’ana komai sun cika sunyi cif-cif dai dai yadda kowanne namiji ya gani zai ƙyasa har zuciyar sa. Sai dai kuma wurin da gizo yake saƙa shine sai anzo ɓangaren kwanciya, ta yadda miji zaiji salam babu armashi a jikin matar.
A takaice dai, macen babu ni’ima a tattare da ita.
Don haka duk macen da take son ta kasance cikin dawwamammiyar ni’ima, to sai tayi ƙoƙari tabi wannan hanyar.
Garin fijil
Garin si’itir
Ruwan albasa
Garin zaitun
Zuma
Zaki samu wadannan kayan hadi sai ki hada su guri guda ki gauraya bayan ki gauraya sai ki zuba zuma ki dunga sha.
Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, suje a saka musu kugun roba. Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan kenan.
Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.
Masana a wannan fannin, sun bayar da shawarwarin amfani da.
– Abarba
– Ayaba
– Gwanda
– Kankana
– Zuma
– Madarar ruwa.
A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa,sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan,mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.
Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.
Allah yasamudace Ameen summa Ameen 🤲🤲🤲.
Kucigaba da kasancewa taredamu akodayaushe dominsamun ingantattun magungunan gargajiya hardama sauran labaran duniya akai akai.