🏥 Magunguna

Hanya mafi sauki da za’abi domin magance matsalar ciwon sanyi dake damun Mata sanyin mara kalli yaddazakayi

Hanya mafi sauki da za’abi domin magance matsalar ciwon sanyi dake damun Mata sanyin mara kalli yaddazakayi

 

Kusan kaso saba’in daga cikin jinyoyin da suke damun mata a fanni ko bangare daya shafi al’aurar su ciwon sanyi ne yake kawo su. Wannan shine dalilin dake tilasta mata da yawa yin amfani da maganin sanyi, musamman ga wadanda suka san koma baya da sanyin ke haifarwa.

 

Kasantuwar sanyi yana da illa sosai musamman a jiki da kuma lafiyar mata, hakan yana da matuƙar tasiri ta hanyoyi da dama, da kuma mabanbanta. Hakan tasa muka ga ya dace mu wayar wa mutane kai game da hanyar da zasu bi wajen magance matsalar su.

Mata da yawa suna ƙorafi akan, ko kuma sakamakon fitar ruwa ta gaban su, wanda wasu lokutan yana zuwa da wari sosai, duk da yake babu zafi lokacin da yake fita. Amma kuma alama ce daga cikin alamun sanyin mara, wanda akasari ya fiya bayyana a garesu.

 

To, ga duk macen da take son magance wannan damuwa, sai ta nemo abubuwa kamar haka;

1 Tafarnuwa
2 Saiwar kanunfari
3 Garin kistul hindi
4 Saiwar zogale

Yadda ake wannan haɗin shine:

Kamar dai yadda kika sani tafarnuwa tana bada kariya sosai ta bangaren abinda ya shafi sanyi da dukkan nau in sa, haka shima kununfari yana da nasa gudunmawar babba.

Saiwar zogale kuwa da garin kistul hind idan dai kina amfani da maganin gargajiya, to tabbas ba sai an fada miki muhimmancin da yake dashi ba. Hasali ma sai dai ki fadawa wani.

 

Don haka zaki samu tafarnuwa mai kyau ki jajjagaz, sai ki hadashi da sauran kayan hadin ki tafasa a cikin tukunya mai kyau. Bayan ya huce sai ki tace ruwan (da rariya ko wani abinda ake tacewa) a cikin kofi ko wani abu da zaki zuba shi ciki wanda anan ne zaki dunga sha har lokacin da zai kare.

In sha Allah za kiga abin mamaki.

Allah yasa mudace.

Ameen Ameen.

 

Kucidakasancewa atareda,akodayaushe domin samun ingantattun maganin sanyi dana karfinmaza.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button