Duk macen da take son ta gyara nononta sannan kuma ta taso da nononta to ga hanya mafi sauki da da zata bi.
Matsalar zubewa ko kuma yakushewar nono abu ne na musamman da yake addabar mata a wannan lokaci, duba da dalilai masu tarin yawa dangane wannan al’amari.
A yau zamu kawo muku hanyar da zaku bi domin ganin kun dawo da martabar sa.
zaki nemi kayan hadi kamar haka;
Hulba
Waken soya
Gyada
Ga Bayani dalla dalla kan yadda za’a haɗa;
Waɗannan kayan haɗi ana niƙasu ne suyi laushi sosai da sosai, sannan a sai haɗa su wuri guda.
Bayan haka kuma za’a rinka shan su tare da madarar gwangwani ta ruwa kamar Peak, ko kuma Olympic, kodai duk wadda ta samu.
InshaAllahu za’a samu kyakkyawan sakamako.
Da yawa yawan mutane (musamman mata), suna korafi akan zafi da suke ji a lokacin jima’i ko kuma lokacin da ba’a jima’i dasu.
Wannan babbar damuwa ce da mafi yawan lokaci kan addabi ni’imar mace, da kuma hanata sukuni sosai.
Idan mace tana fama da wannan al’amari, akwai abubuwan da ake yi don ganin an rabu dashi na har abada.
Duk mai fama da wannan matsalan zata nemi kayan hadi kamar haka:
– Garin Ganyen kabewa.
– Garin Ganyen zogale.
– Man kadanya
– Garin Majigi.
– Garin Hulba.
Yadda Zaki Hada Wannan Sirri Shine :
Zaki samu kayan hadin sai ki hada su guri guda ki kwaba da man kadanya sai ki dunga shafawa sau uku a rana, duk shafawa sai ki wanke da ruwan dumi zakiyi mamaki kwarai.
Idan Nonuwan ki kanana ne kina so su zama manya kamar yadda kike so dai-dai kina iya yin wannan hadi domin samun lafiya nononki.
Abubuwan da zaku nema domin hada wannan maganin sune kamar haka.
(1) – cukwul.
(2) – Ogarin alkama.
(3) – Aya.
(4) – Nonon saniya.
(5) – Madara.
(6) – Garin hulba.
(7) – Cukwul.
Isan kun samo wadannan abubuwan ga yadda zaku hada su.
Idan kin samo Cukwal mai dan yawa sai ki kawo garin alkama gwangwanin daya, sai Aya itama gwangwani daya, sai ki daka su zasu zama gari ki tankade ki samu Nonon saniya.
idan kuma bakya shan Nonon saniya ki sami madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 ki dama, sai kina shan kullum sau daya.
Sannan ki Lura lokacin da zakiyi wanka kitafasa ruwa da garin hulba a ciki ki bari yayi sanyi sai ki wanke Nonuwan naki da shi sannan Kiyi wankan.
Matar aure ko Bazawara ko Budurwa zasu iya yin wannan hadin maganin.