🏥 Magunguna

Dalilan da kuma abubuwan da suke sanya rashin gamsarwa a tsakanin ma’aurata a lokacin saduwa

Dalilan da kuma abubuwan da suke sanya rashin gamsarwa a tsakanin ma’aurata a lokacin saduwa

Dalilan da kuma abubuwan da suke sanya rashin gamsarwa a tsakanin ma’aurata a lokacin saduwa

 

 

Lokuta da dama abinda yake hana samun gamsuwa a tsakanin iyali suna da matukar yawa, tun daga cututtuka dake damun ma’aurata wadanda ba tare da saninsu ba har zuwa wadanda suke sane dasu amma anyi buris an kyalesu.

 

 

To maida hankali shine babban abinda yafi dacewa ayi, domin gudun zuwan wani lokaci da zai kasance ana son ayi jima’in amma abin yafi karfin ku.

 

 

Anan zamu kawo muku kadan daga cikin abubuwan da suke hana jindadi da kuma sukuni wajen tabbatar da ma’aurata sun samu damar yin jima’i yadda ya kamata har kowa a cikin su yaje mawar gamsuwa.

 

Dalilan kuwa sun hada da:

 

 

Na farko (1): Haifar da kwayoyin cuta (Infection) da za su baibaye al’aurar mace wadanda za su iya kara hadarin jawo nakuda tun lokacin haihuwa bai yi ba, da kuma hadarin saurin kamuwa da cututtuka masu alaka jima’i kamar ciwon sanyi da sauran su.

 

 

 

Na biyu (2) Yana iya jawo kwayoyin cuta ga mahaifa da kwayayen haihuwa da aka fi sani da Pelvic inflammatory disease (PID). “Wannan al’amari na iya hana mace samun haihuwa kwata-kwata, ko kuma ya sa mace ta dinga daukar ciki a wajen mahaifa,” in ji Dakta Hauwa.

 

 

 

Na uku (3) Wata mujallar lafiyar mata ta Amurka ta intanet WebMD, ta ce wani bincike da aka yi ya gano cewa mata masu wanke al’aura da sabulu ko sinadarai sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar PID.

 

 

Na hudu (4) Akwai kuma yiwuwar mace ta dinga fama da matsanancin kaikayi a gabanta, ko kuraje su fito mata ko kuma al’aurar ta dinga tsagewa.

 

 

Na biyar (5) A wasu lokutan wani ruwa mai kauri mai kalar dorawa ko kore mai kuma wari zai ta fitowa daga gaban mace, wanda dole sai ta je asibiti don a magance shi.

 

 

Kamar yadda muka kawo muku yadda za’a hada maganin sanyi a baya, a yau ma wata faida wacce take maganin sanyi na jiki dana mara.

 

 

Zaku samo wadannan abubuwan kamar haka.

 

1 Furen Zugale.
2 Albasa.

 

Yadda Za’a Hada :

 

 

Za’a samu furen Zogale a wanke sai a samu Albasa a yayyanka a hada da furen a dafa,idan aka sauke ya wuce sai a rika sha kamar shayi safe da yamma.

 

 

Zakuyi wannan hadin maganin har na tsawon sati daya, ko kuma ana yin amfani da wannan hadin har tsawon sati 2, amma kafin a fara ganin aikin sa, sai anyi tsawon kwanaki 3 zuwa Kwanaki 5 ana sha, domin yana bin jiki ne.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button