🎬 Hausa Series Fim

Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa ‘Yan Kasa

Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa 'Yan Kasa

Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa ‘Yan Kasa

 

Kasar Saudiyya ta bai wa kasar Najeriya kyautar dabino har tan 50 don habaka hulda tsakaninsu

 

Jakadan kasar a Najeriya, Faisal Alghamdi shi ya ba da kyautar a madadin kasar Saudiyya a Abuja.

 

Kyautar an ba da ita ne ta hannun daraktan yanki a ma’aikatar kasashen waje, Janet Osita a Abuja.

 

FCT, Abuja – Kasar Saudiyya ta gabatar da kyautar tan 50 na dabino mai inganci ga kasar Najeriya don kara habaka hulda tsakanin kasashen biyu.

 

Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Faisal Alghamdi shi ya ba da kyautar a madadin kasar Saudiyya a yayin wani biki a Abuja.

 

Da yake mika kyautar, shugaban tawagar KSRelief, Nezat Talaqi ya ce kyautar daga mai kula da masallatai masu tsarki guda biyu na Sarki Salman Al Saud ne.

 

Ya bayyana irin taimakon da suke bai wa Najeriya

 

Ya ce gwamnatin kasar Saudiyya karkashin hukumar tallafi da agaji ta KSRelief tana ba da tallafi ga gwamnatin Najeriya, cewar Daily Nigerian.

 

Ya kara da cewa taimakon kwanan nan da hukumar ta yi shi ne bai wa mutane 48,300 Kwando cike da abinci a jihohin Kano da Yobe da kuma Borno akan kudi $500,000, cewar rahotanni.

 

Acewarsa..

“Ba da wadannan dabinai na daga cikin tallafi da kuma taimako daga mai kula da masallatai masu tsarki guda biyu, Allah ya kare shi.

 

“Muna ba da taimakon ga kasashen da muke da kyakkyawan alaka da su wandanda Najeriya ke ciki don mutane masu bukata.

 

“Wadannan da wasu yana tabbatar da yadda kasar Saudiyya ke kara inganta mu’amala tsakaninsu da Najeriya a dukkan matakai.

 

”Sannan za mu ba da magani kyauta ga ýan Najeriya nan ba da jimawa ba a jihohin Kano da Lagos da sauransu.

 

Kamar Kullum: Saudiyya Ta Ba Wa Najeriya Kyautar Dabino Tan 50 Don Raba Wa ‘Yan Kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button