HAJJI 2023: Gwamnatin Filato ta bar mahajjatan jihar su na hajijiya a Madina
Maniyyata aikin Hajjin 2023 daga Jihar Filato su bayyana cewa sun shiga damuwa, saboda tun bayan saukar su Saudi Arabiya, babu jami’an kiwon lafiya ko jami’an kula da mahajjata ko ɗaya tare da su.
Premium Times ta fahimci cewa jami’an kiwon lafiya da masu kula da mahajjata daga Jihar Filato, tilas su haƙura su zauna a Najeriya, saboda gwamnatin da ta sauka a farkon wannan mako, ba ta saki kuɗaɗen ɗawainiyar ayyukan Hajji ba kafin ta miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin PDP a jihar ba.
Majiya ta ce rashin ɓangarorin jami’ai har guda uku tare da maniyyatan Filato a Makka da Madina, zai iya haifar da gagarimar matsala, ko kuma a ce ruɗani.
Domin hakan zai haifar da rashin samun kulawa gare su a fannin lafiya, ɓangaren abinci da kuma masu nunnuna masu yadda ake gudanar da wasu ayyukan ibada ko zuyarce-ziyarce.
Su dai jami’an Hukumar Jin Daɗin Alhazai su ne ƙashin bayan samun nasarar aikin Hajji a kowace jiha.
A na so kowace jiha ta tura tawagar likitoci da jami’an kiwon lafiya, masu nuna wa maniyyata wurare da yadda ake ibada, malamai masu wa’azi da jami’an kula da abinci da rarrabawa da sauran su.
Wani maniyyaci da ya tafi a ranar Juma’a, ya shaida wa wakilin mu cewa lamarin na su na neman dagulewa domin nan da ‘yan kwanaki za su kammala ziyarar da su ke yi a Madina, kuma a ranar za su wuce Makka.
Ya ce wani maniyyaci ya samu ciwon farfaɗiya a cikin jirgi, kan hanyar su ta tafiya Madina daga Najeriya. Ya ce abin baƙin ciki da tausayi, aka rasa jami’an kiwon lafiya da za su duba shi.
“Sai a lokacin ne mu ka fahimci ashe ba mu tafi da jami’an kula da jin daɗin alhazai ko ɗaya ba daga Filato. Kawai dai an bar mu mu kaɗai sai gagaramba mu ke yi.”
“A jiya mahukunta su ka ce mana gwamnatin Jihar Filato ce ba ta saki kuɗaɗen da ya ma’aikatan kula da masu aikin Hajji ba. Sai aka ce mana mu koma gida kawai.” Haka wani malami ya shaida wa wakilin mu a hirar da ya yi da shi ta waya daga Madina.
Ya ce akwai matsala, saboda maniyyata da yawa ba su san sharuɗɗa da farillan aikin Hajji ba, ba su ma san yadda ake aikin Hajji ba.” Inji malamin.
Allah yasamudace yafitardamu dagacikin wannan kangin narayuwa.
Kucigaba da kasancewa taredamu akodayaushe dominsamun ingantattun magungunan gargajiya hardama sauran labaran duniya akai akai munagodiya dasauraranmu dakuke akodayaushe.