Allah Sarki: Murja Ibrashim Kunya da Moofy mawakiya sun nuna alhinin mutuwar Kamal Aboki
Allah sarki murja Ibrashim Kunya da Moofy mawakiya sunyi alhinin rasuwar Kamal Aboki.
A wata bidiyo da muka samu wanda Tashar “Duniyar Kannywood” suka bayyana munga Murja Kunya tana kuka har da shashsheka tana cewa duniya ba komai bace, domin kuwa mutuwar Kamal Aboki ta girgirzata.
A bangaren Moofy mawakiya ita ma kuka take tana bayanin abubuwan da suka yi da Kamal Aboki lokacin da yana raye.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin jin bayanin Moofy mawakiya da kuma nuna alhinin da Murja Ibrashim Kunya tayi kan rasuwar Kamal Aboki.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.
https://youtu.be/38GfB7DtdrI
Allah yajikansa yagafartamasa.
Allah Sarki: Saurari wani bayanin sirri da Murja Kunya tayi bayan kamata da aka yi
Yanzu haka dai fitacciyar yar tiktok murja Ibrahim kunya tana gidan gyran hali akan bidiyo da take yi a manhajar Tiktok da akwai zage zage da kuma kalamai wadanda basu dace ba tana furtawa a matsayinta na ya mace musulmi kuma bahaushiya.
Domin kuwa al’adar malam bahaushe Akwai kunya da kamunkai musamman ga ya mace shafin hausamini ya tattaro mana wasu bayyanai da ke cikin faifan bidiyo.
Allah Sarki! Abin Tausayi, Cikin Kuka, Jawabin Murja Ibrahim kafin A Daure Ta Abin Da Yasa Ta Zargi Me Wushirya Da Najamu, Murja Ibrahim Din Shahararriyar Yar Tiktok Ta Fashe Da Kuka. Kan Cin Amanar Da Babban Abokinta Da Kuma Qawarta Su Mata.
Zuwa Yanzun Dai Murja An Turata Gidan Gyara Hali, Inda Ake Zarginta Da Qazafi Da Tayiwa Idris Mai Wushirya Tare Da Aisha Najamu.