Sati mai zuwa jarumar shirin Izzar So Karima za’a daura aurenta da mawaki Izzudden
Sati mai zuwa jarumar shirin Izzar So Karima za’a daura aurenta da mawaki Izzudden

Sati mai zuwa jarumar shirin Izzar So Karima za’a daura aurenta da mawaki Izzudden
Yanzu haka shirye-shiryen shagalin auren ‘yan masana’antar Kannywood biyu ya kankama inda za’a daura auren jaruma Khadija Yobe wacce aka fi sani da Karimar a cikin shirin Izzar So da mawaki Izuddeen M. Doko, kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwaito.
Jarumar ta samu karbuwa ne sakamakon shirin fim din Izzar So mai dogon zango wanda kowa ya santa.
Kuma ana matukar yaba mata kan yadda take shigar mutunci da kuma mu’amala mai kyau tare da abokan sana’arta.
Kamar yadda Mujallar Fim ta bayyana an fitar da hotunan da masoyan suka yi kafin aure wanda mutane da dama suka dinga yi musu fatan alkhairi bayan ganinsu.
Za’a daura auren ne a ranar Juma’a 10 ga watan Fabrairun 2023 a dai-dai masallacin Juma’a dake anguwar Nasarawa a garin Damaturu babban birnin Jihar Yobe.
Ana sa ran daurin auren na rana ne don kamar yadda katin ya nuna, za’a daura ne karfe 2 dai-dai, Allah ya sanya alkhairi kuma ya ba da ikon halarta Ameen.
Allah yabada zaman lafiya yasan alkairi acikin auren ameen summa Ameen.