Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano
Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano

Kisan Ummita: Ba da niyyar kisa na daɓa mata wuƙa ba, in ji ɗan China da ya hallaka budurwarsa a Kano
Wani dan kasar China mai suna Frank Geng Quangrong mai shekaru 47, a yau Alhamis ya tabbatarw wata babbar kotu a Kano cewa ya daɓa wa budurwarsa ‘yar Najeriya mai suna Ummukulsum Sani wadda aka fi sani da Ummita wuka.
Wanda ake tuhumar, wanda ke zaune a Railway Quarters Kano, na ci gaba da gurfana ne a gaban kotun bisa laifin kisan kai.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito Frank da lauyan masu gabatar da kara ke yi masa tambayoyi, Darakta mai shigar da kara na jihar Kano, DPP, Aisha Mahmoud, ya shaida wa kotun cewa a wannan ranar da ibtila’in ya afku, abubuwa da dama sun faru.
Ya shaida wa kotun cewa ya zo Najeriya ne a 2019 domin yin aiki a matsayin Manajan Kasuwanci da Tallace-tallace a Kamfanin BBY Textile Kano.
“Ana biya na Naira miliyan 1.5 duk wata kuma ina yin wasu harkokin daban-daban. A ranar da kaddarar ta afku, Ummukulsum ta tura ni kan gado.
“Na caka mata wuka ne ba tare da niyyar kashe ta ba.
“Na fita daga dakin ta taga tunda an kulle kofa daga waje ina so in kai Ummukulsum ɗin asibiti amma sai ‘yan sanda suka iso suka kama ni,” in ji Mista Frank.
Karanta wannan👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Jarumi Ne Kadai Zai Iya Abinda Shugaba Buhari Ya Yi A Yau
Daga M Inuwa M.H
Hakika wannan magana ta shugaban kasa Muhammad Buhari ta birge ni, kuma wannan magana ta saka ni farin ciki da annashuwa a daidai lokacin da na ji shugaba Buhari na caccakar kasar Myanmar akan kashe musilmin Burma.
Sai da na ji kamar na hadiye shi don murna. Wannan shine shugabanci nagari ka fito a taron duniya ka fadi ra’ayinka ba tare da tsoro ba. Wannan jarumta ce.
Allah ya saka maka da alkairi, ysa ka gama mulkin ka lafiya, ya kara maka lafiya.
Shugaba mai karfin hali ba shi da cikakkiyar lafiya, amma ya sadaukar da kansa ga al’umma. Wannan shine shugaba abin tunawa a tarihin Nijeriya.
Muna maka kyakkyawan zaton samun nasarar cikawa Nijeriya alkawarin da ka dauka Baba Buhari.
MH ISMOG
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Allah yasamudace Ameen summa Ameen 🤲🤲🤲.