.
📻 Labaran Hausa

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Wani bidiyo na jarumar Nollywood, Mercy Aigbe tana mai sake gabatar da kanta a sabon addininta ya yadu.

An yi hira da ita ne a wani taron Ramadan da jarumar ta shirya tare da mijinta wanda ya samu halartan manyan jarumai.

Bidiyon wanda tuni ya yadu ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.

Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana’a da yan uwa zuwa taron Ramadan.

Jaruma Mercy Aigbe ta musulunta

Bayan nasarar da ta samu a taron, an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da cewar ta bar addinin kirista zuwa na Musulunci.

A bidiyon, an iya gano jarumar tana sake gabatar da kanta da sunayenta da suka hada da na Musulunci.

“Sabon sunana shine Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah.”

ladyrealtorzinnie:

“Ina fatan ba za a ji labari daban ba anjima idan sabuwar mata ta shiga saboda….”

l.tobiloba:

“Ban taba ganin barauniya mai alfahari ba. Ina fatan za ki ci gaba da wannan karfin halin idan sabuwar mata ta shigo.”

i_am_nova_kae:

“Za ka yi tunanin wasu matan za su fi hikima amma soyayya sa’anka ne?”

david_chibuzo_690:

“A kan mijin wata.”

Allah yasa mudace ameee summa ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button