.
🏥 Magunguna

Maganin karfin mazakuta kankancewar gaba karin ruwan maniyyi da saurin kawows

Maganin karfin mazakuta kankancewar gaba karin ruwan maniyyi da saurin kawows

Maganin karfin mazakuta kankancewar gaba karin ruwan maniyyi da saurin kawows

Yan uwa barkan mu da wannan lokaci a yau ma kamar kowacce rana na sake dawowa akan dai matsala wacce a yanzu itace take damun ma’aurata maza na wannan zamani, ina magana ne akan rashin kuzari karashin karfin gaba da saurin inzali karancin maniyyi da kuma sanyin mara.

Amma kafin bayani akan magani kamar yadda wasu lokutan ina fada cewa ba iya Cututtuka ne da ake yawan fada ba suke jawo irin wadannan matsalolin ba, akwai sha’ani na zamantakewar aure indai kana samun matsala tsakaninka da iyalin ka a wani bangare na zaman aure hakan yana tasiri wajen jawo a karshe ka dena sha’awar iyalin naka kwata kwata.

Sannan akwai gajiya ba yadda za’ai lokacin da kake son ka kusanci iyali kaje musu da gajiya kuma kace za’ ayi abun kirki, dole sai an nutsu an huta hankali ya kwanta komai yayi dai-dai kafin kace zaka fara wani sha’ani, yin jima’i da gajiya babu abinda za’a samu sai rashin gamsuwa.

Akwai damuwa ko bacin rai ko yawan tunani na rayuwa ko kasuwanci suma duka suna bawa da Namiji gudan mawa wajen jawo masa tabarbarewa a sha’anin zamantakewar aure wajen raba masa nutsuwa da Hankali wajen samun jin dadi da abinda yake na sha’anin kula da iyalin sa.

Sannan akwai su kansu Cututtuka wadan da ake fada dama wadan da ba’a fada sabida rashin bincike na wasu sai dai kaji ana ta cewa, sanyi basir kowanne lokaci kayi ta karbar magani amma babu sauyi.

Cututtukan kuwa sune kamar haka.

(1) Hawan jini.

(2) Ciwon suga.

(3) Ciwon hanta.

(4) Ciwon koda.

(5) Cutar da take iya taba laka.

(6) Ciwon Damuwa.

(7) Cutar Prostate.

(8) Cutar da suke kama kwakwalwa.

Wadan nan sune kadan daga cikin Cututtuka wadan da ba kowannne lokaci ake fara su a matsayin Cututtuka da suke jawo rauni a bangaren sha’anin zaman aure ba.

Amma ga wani hadi don magance wannan sha’ani in sha Allah wanda yaki aiki koda kana da akasarin abubuwan da aka lissafa in sha Allah zaka dace idan kayi amfani da shi.

Abubuwan da zaku nema sune kamar haka.

(1) Zuma.

(2) Tafarnuwa.

(3) Citta.

(4) Lemon tsami.

Da farko zaka samu citta kamar guda daya a rana ta biyu, sai ka samu tafarnuwa silin ta guda 5 ma’ana ‘yan kananan guda 5 sai ka samu lemon tsami daya a raba shi 3 ka dauki kashi daya.

Idan kayi haka, ga yadda zaka hadasu.

Zaka daddake kowannen su sai ka samu ruwan zafi wanda ya tafasa a zuba akai ruwan kamar kofi 1 a matsa lemon tsamin a ciki, sai ka barshi yayi kamar minti 10 sai a tace a zuba zuma chokali 2 a ciki sai ka shanye wannan hadin, kamar awa guda kafin a kusanci iyali.

In sha Allah kayi tsawon sati 2 kana yin wannan hadin zaka dawo cikakken Namiji wanda uwar gida zata rika girmamawa da ganin kima da mutuncin sa a kowanne lokaci.

Allah yasamudace Ameen Ameen 🤲🤲.

Kucigaba da kasancewa taredamu akodayaushe dominsamun ingantattun magungunan gargajiya hardama sauran labaran duniya akai akai munagodiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button