.
📻 Labaran Hausa

“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa

“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa

“Aiki Ya Yi Kyau”: Uba Ya Samo Dabarar Shayar Da Dansa a Bayan Idon Mahaifiyarsa

 

Wani bidiyon TikTok da ke nuna wani uba yana shayar da dansa cikin dabara ya tsuma zukata da dama.

 

A bidiyon, uban ya sanya hoto da ke dauke da fuskar mahaifiyar yaron a nashi fuskan sannan ya makala fida a kirjinsa.

 

Karamin yaron da ya fada tarkon mahaifin nasa ya sha madarar nasa hankali kwance yana mai tunanin da gaske mahaifiyarsa ce ke shayar da shi.

 

Wani uba ya shirya wata dabara don tabbatar da ganin cewa karamin dansa ya karbi abincinsa a bayan idon mahaifiyarsa kuma hakan ya haifar da martani masu yawan gaske.

 

A bidiyon da ya yadu, mahaifin yaron ya dauki babban hoton fuskar matarsa sannan ya makala a nasa fuskan inda ya kuma dauki fidan yaron ya sakala a kirjinsa don nuna cewa ruwan nono ne ke fita daga jikinsa.

 

Alamu sun nuna yaron bai fahimci wayon da aka yi masa ba domin dai ya mayar da hankali wajen tsotson fidansa.

 

Karamin yaro ya fada tarkon mahaifinsa

 

Ga dukkan alamu, ta wannan hanyar ne kadai yaron zai karbi madararsa a bayan idon mahaifiyarsa.

 

Masu amfani da TikTok da dama da suka kalli bidiyon sun yaba ma kokarin uban kuma sun ce za su yi amfani da irin haka.

 

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, bidiyon ya tattara ‘likes’ fiye da 100,000 da martani fiye da 1000 a TikTok.

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button