Advertisement
🏥 Magunguna

Yadda zaka gano mazakutar ka tana aiki yadda ya kamata ko ta mutu koda baka da aure

Yadda zaka gano mazakutar ka tana aiki yadda ya kamata ko ta mutu koda baka da aure

Advertisement

Yadda zaka gano mazakutar ka tana aiki yadda ya kamata ko ta mutu koda baka da aure

Yan uwa da dama suna tambaya shin taya ne ake gane cewa Azzakari yana lafiya ba tare da an kusanci mace ba,to insha Allah ayau maijalalainitv.com zata kawo muku hanyoyi da zaku iya gane hakan.

Da yawa daga yan uwa suna damun kansu tare da daga Hankali cewa suna tsoron kada suyi aure su kasa biyawa mace bukatar su,ta hakan wasu suke fadawa zinace zinace domin wai su samu gamsuwa kafin suyi aure.

Wanda shi kansa damuwa da cewa kana da matsala ko baka da ita zai iya jefa ka cikin wani yayi da wani hali mara dadi,saboda haka a rika tambayar abu idan baa sani ba.

Da farko abubuwan da zakai duba dasu domin ka gane cewa baka da wata Matsala kuma mazakutar ka tana cikin koshin lafiya shine duba da wadan nan abubuwa.

(1) Ganin fitar farin ruwa a lokacin fitsari.

(2) Jin zafi ko suga ko kaikai ko ciwo a cikin kwarkwaron mazakuta.

(3) Ganin jini ko zare zare a cikin fitsari.

(4) Ganin kuraje akan mazakutar ka.

(5) Gaban ka yayi wata kala sabanin yadda kalar sa take,dukda dama mazakuta tana da duhu fiyevda fatar jiki.

(6) Ga masu aure akwai jin zafin gaba a lokacin saduwa ko bayan saduwa.

Daga cikin alamomin nan da muka bayyana akwai alamomin ciwonn sanyi na bacterial infection kamar su gonorrhea Chlamydia Hpv Virus da sauran su,wanda suna daga cikin abubuwan da suke jawo mazakutar mutum ta samu matsala.

Bayan wadan nan akwai wasu abubuwa da suke jawo kaga gaban ka kamar baya aiki sune.

1. Kiba mara musaltuwa.

2. Ciwon suga.

3. Hawan jini.

4. Damuwa.

5. Wasu daga ciwon zuciya.

Sannan yin masturbation da yawa wato istim’nai shima yana jawo Azzakari ya samu matsala mai girma.

Hanyoyin da zaka bi ka zauna da mazakutar ka lafiya kalau.

1. Dena shaye shayen Taba da Giya.

2. Yawan motsa jiki.

3. Daidaita abinci.

Sannan idan baka gane wani abu ba ka tuntubi likitan ka cikin gaggawa ko kuma idan kaga wata alama da muka bayyana.

Allah yasamudace Ameen summa Ameen 🤲.

Kucigabadakasancewa taredamu akodayaushe domin samun ingantattun magungunan gargajiya hardama sauran labaran duniya akai akai munagodiya dasauraranmu dakuke akodayaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button