Yadda Ake Kara Girman Azzakari A Saukake
A wannan makala za mu kawo muku yadda za ku kara girman azzakarinku, idan mu ka ce girman azzakari mu na nufi, kauri da tsawon azzakari. Kodayake, Allah(S.W.T) Ya halicci maza gwargwadon nau’in mazakutarsa kuma da hakan ne kowa zai iya biyan bukutar jima’i ga matarsa.
Kauri da tsawon azzakari wani sanadari ne na gamsar da iyali. Sai dai a wasu lokutan akan samu rigingimu tsakanin ma’aurata saboda yadda wasu mazan ba sa iya biya wa matansu bukatar auren, har hakan kan kai ga rabuwa.
Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa, Allahu(S.W.T) Ya bambamta maza wajen halittar mazakuta haka kuma Ya bambamta mata wajen halittarsu. Saboda haka ne, bukatarsu ta bambamta ta fuskar jima’i, inda wasu matan ke son namiji mai girman azzakari kafin su biya bukata.
Sakamakon irin halittar da Allah ya yiwa wasu matan, ba sa samun gamsuwa daga namiji har sai sun samu, mai girman azzakari ko kuma mai tsawo da zai cika su, ko kuma ya kai makurar farjinsu su ji kamar za su yi amai.
Masana sun ce, wasu matan Ubangiji Ya halicce su da zurfi ko fadin farji ta yadda idan azzakarin mutum gajere ne ko kuma ba shi da kauri to da wahala ya iya biya wa irin wadannan mata bukata ta fuskar jima’i. Irin wadannan mata kan samu gamsuwa ne kawai idan sun yi arangama da mai girman azzakari. Wannan dalili ya sa mu ke son nuna mu ku yadda ake kara girman azzakari, wato yadda ake kara kauri da tsawon azzakari a saukake.
Sai daia a gefe guda wasu manazarta na ganin babu wata alaka tsakanin biyan bukatar jima’i da girma ko rashin girman azzakari. Amma a gaskiya wannan ra’ayi bai samu karbuwa ba wajen akasarin wadanda su ka yi zanarce-nazarce a wannan janibi.
Mujalla ta bata lokaci mai yawa wajen bibiyar zanarce-nazarce ma su tarin yawa kan wannan mas’ala, sai mu ka yanke shawarar sanar da ‘yan uwa yadda za su kara girman azzakarinsu don kara samun dankon zamantakewar aure, ba don komai ba, sai don mun yi amanna da abin da Hausawa ke cewa, “Idan ka na da kyau ka kara da wanka”. Sakamakon haka mu ka yi wa wannan makala taken “Yadda ake kara girman azzakari a saukake”.
Yadda Ake Kara Kauri Da Tsawon Azzakari.
Kamar yadda mu ka ambata a sama cewa, masana a wannan fanni sun gudanar da bincike mai zurfi kuma sun samar da hanyoyi da yawan gaske da za a iya kara kauri da tsawaon azzakari, (Yadda za a kara girman azzakari), amma mun zabi wasu hanyoyi guda biyu dangane da wannan makala. Mun zabi wadannan hanyoyi biyu ne kuwa, gannin yadda su ka shahara, don kuwa maza da yawa sun jarraba su kuma sun samu biyan bukata.
Dalili na gaba na zabin wadannan hanyoyi shine, su na da saukin hada wa, kuma kayan hadin na samuwa a kowannne lokaci kuma ga su da araha. Sabosa haka kowa zai iya hada wa a gida ba tare da wahala ba, kuma ya kara girman azzakarinsa.
Hanya Ta Farko:
Ana hada wannan maganin karin kauri da tsawon azzakari ne da abubuwa biyu kacal: Su ne nama da kuma zuma.
Yadda mutum zai hada wannan magani shine, ya samu namansa marar kitse ko kuma mu ce jan nama. Sannan sai ya tanadi zumarsa mai kyau marar hadi.
Bayan ka kammala takidar wadannan kayan hadi na ka, sai mu je ga yadda za a hada. Tun da farko sai ka yanka naman nan yanka-yanka gwargwadon yadda mahauta ke yanka wa ma su abinci naman sayarwa, amma zai yi kyau kar yankan ya kasance kanana sosai, sai ka soya naman, amma ka lura da kyau kar ya kone, don gudun kar a rasa wasu sanadarai ma su muhimmmanci.
Bayan ka kammala soya naman nan sai ka zuba shi cikin ruwan zumarka da ka tanada tun da farko, sai ka adana a mazubi mai kyau. Kullum da dare sai ka dinga cin naman nan yanka daya. Da ikon Allah za ka sha mamaki.
Wannan hadi an jarraba shi kuma an samu biyan bukata, don haka mai karatu ka gwada za ka yi ma na addu’ar alkhairi daga bisani, in sha Allahu. Wannan shine hanya ta farko yadda ake kara girman azzakari a saukake.
ALLAH YASA MUDACE AMEEN SUMMA AMEEN.