.
📻 Labaran Hausa

Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

Sihiri Aka Mun Na Bar Kwankwaso Na Koma Wurin Ganduje, Ali Artwork

 

Fitaccen jarumin Kannywood kuma ɗan wasan barkwanci, Ali Artwork Maɗagwal, ya ce asirce shi aka yi a siyasar Kano.

 

Maɗagwal kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bar Kwankwasiyya ya koma tsagin Ganduje ne sabida an sihirce shi.

 

Ɗan wasan barkwanci yana ta fafutukar mi’ara koma baya zuwa Kwankwasiyya amma abun ya ci tura.

 

Kano – Jarumi kuma mai nishaɗantarwa a Kannywood, Ali Muhammed Idris Artwork, wanda aka fi sani Maɗagwal ya ce ya bar Kwankwasiya zuwa Gandujiyya saboda an masa asiri.

 

Daily Trust ta ce Rabiu Kwankwaso ne jagoran ɗarikar Kwankwasiyya yayin da gwamna Abdullahi Ganduje ke jagontar Gandujiyya a siyasar Kano ta dabo.

 

Dukkan sansanonun biyu sun yi gaba da gaba da juna a zaɓen gwamna ranar 18 ga watan Maris, 2023, inda NNPP ta Kwankwaso ta tumurmusa APC karkashin Ganduje.

 

Yayin da yake martani kan kalaman da magoya bayan Kwankwasiyya ke yi a kafafen sada zumunta, Maɗagwal ya ce asirce shi aka yi.

 

Yan Kwankwasiyya sun bayyana cewa ba zasu karbi tubar Jarumin ba ko da kuwa ya nemi a masa wankan tsarki ya dawo inuwar Kwankwaso bayan NNPP ta ci Kano.

 

 

Sun yi ikirarin cewa Ali Artwork watau Maɗagwal ya musu kalaman rashin kunya har da taɓa Madugun Kwankwasiyya lokacin da ake tunkarar zaɓe.

 

A sahihin shafinsa na dandalin Facebook, Artwork ya ce ya kamata mutane su fahimci cewa ba yin kansa bane asiri aka masa sabida haka ya dace a masa uzuri.

 

“Asiri aka mun, shiyasa na koma ɗayan ɓangaren amma Alhamdulillah na dawo cikin hanyyaci na bayan Addu’o’i da neman magani. Tun asali ni ɗan ɗarikar Kwankwasiyya ne tun 2019.”

 

Maɗagwal ya yi yunkurin komawa wa tafiyar Kwankwasiyya bayan INEC ta ayyana Abba Gida-Gida a matsayin wanda ya ci zaɓen Kano amma magoya baya sun tare ko ina.

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button