DUK BANKIN DA YA KI KARBAR TSUHUN KUDI ZANSA A RUSHE BANKIN SAKON GWANAN GANDUJU
CANJIN KUDI, KA DA KU YARDA DA INGIZA MAI KAMTUN GWAMNAN KADUNA
-CIKIN RAMI ZAI JEFA KU, KAMAR YADDA GANDUJE YA ZUGA ‘YAN KASUWAR KANO.
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El Rufa’I ya ce ya bijirewa umarnin Shugaban kasa Muhammad Buhari na dakatar da karbar naira dubu da naira dari biyar. Ya ce a jiharsa wannan doka ba za ta yi aiki ba. A don haka, ya ce jama’ar jiharsa su cigaba da karbar kudaden. Gwamnan ya ce matakin Shugaban kasa, matakin hana zabe ne da kafa gwamnatin wucin-gadi.
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Bjamiliya shi ma ya nuna kokawarsa kan wannan mataki na shugaban kasa. Shi kuma dan Majalisar wakilai Alasan Ado Doguwa daga jihar Kano, ya je fadar Shugaban kasa afujajan, ya ce shi fa naira miliyan saba’in ya ke nema domin gudanar da harkokinsa a lokacin zabe.
Fitaccen lauya Femi Falana ya ce matakin shugaban kasa zai sake jefa al’umma cikin matsi, domin babu isassun naira dari biyu da aka ce a cigaba da amfani da su.
A jihar Kano kuma, jim kadan bayan jawabin Shugaba Buhari, mutane sun cika babban bankin kasa CBN da kudade cike cikin buhuna da leda na tsoffin kudade. Sun ce Gwamna Ganduje ne ya zuga su ya ce su ci gaba da karbar tsoffin kudade. Ya yi barazanar tsaya musu, kuma har ya rufe wasu wurare da su ka ki karbar tsoffin kudaden. Amma tun bayan jawabin Shugaban kasa, ba abin da ya tsinana musu, bayan ya ingiza su, sun yi ta karbar tsoffin kudaden.
Yanzu dai ‘yan kasa sun soma daukar darasi, daga wasan ball da Shugabannin Najeriya ke yi da su. Yanzu Nasir El-Rufa’I ya ce mutanen jihar su cigaba da karbar kudade. Tambaya anan ita ce, idan sun cigaba da karbar kudaden, Gwamna kana da bankin da za su kai a canza musu da sabbin kudade? Ko kuwa kana da sabbin kudaden ne gidan gwamnati da za su shigo su yi layi ka canza musu kudaden?
Cika bakin Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya isa darasi. Bayan ya ingiza mutane sun cigaba da karbar tsoffin kudaden, ga shi jawabin Shugaban kasa ya rusa maganarsa.
Maganar kudaden kasa, karbar su ko rashin karbar su ba a hannun Gwamnoni ya ke ba, yana hannun Gwamnatin tarayya ne karkashin Shugaban kasa. A domin haka, duk wani Gwamnan da ya ingiza ku, cigaba da karbar sabbin kudade ingiza mai kamtu ruwa ne kawai. Gwamnonin da su ke ingiza a cigaba da karbar tsoffin kudaden neman goyon bayan siyasa ne daga gafalallun talakawa.
Mutanenmu dai an bar shiri tun rani. An jibge kudi a gidaje shekara da shekaru, an ki bin tsari na zamani na kai kudade banki. Sannan kuma, duk da tsawon lokacin da aka bada, mutane sun yi biris sai da lokaci ya kure su ka soma rububin zuwa banki.
Shawara musamman ga jama’ar jihar Kaduna, ka da ku yarda da ingiza mai kamtun Gwamna El-Rufa’I, na cigaba da karbar kudade. Ba abin da zai tsinana muku. Mutumin da ya karya ku, ya kwance muku zani a kasuwa, shi ne ku ke tsammanin zai tsaya muku ka da ku yi asarar kudade? Idan ku ka cigaba da karbar tsoffin kudaden, ranar da ElRufa’in ya goce ya bar ku da tarin takardun tsoffin kudade, za ku ce na gaya muku.
Bala M Makosa
(Baban Haidar)