Hanyar da Mace zatabi idan tanason kugunta yu kara girma sosai
Idan mace tana son kugunta ya girma sosai ya kara fadi da budewa, abu ne mai saukin gaske matukar za’a bi matakai wadanda suka kamata. Wannan matakan basu da wata matsala ga lafiya ko kuma sauyi na tunanin dan adam da zai jawo dana sani a gaba.
Girman kugu yana daga cikin abubuwan da suke jan hankalin maza domin shi kansa kugun cikar sura ne na mace, haka zalika yana nuni da mace zata iya gamsar da namiji a lokacin da yake yin jima’i da ita.
Wannan tasa mata da yawa musamman wadanda suke da shi suke yin alfahari da nuna kansu a wurare da dama kamar taro (watakila taron daya kunshi mata da maza) saboda da hakane wani zai gani sannan ya kyasa.
Ina son a fahimci cewa girman kugu halitta ce, wasu matan har kauce hanya suke yi, suje a saka musu kugun roba. Kun ga akwai alamar kauce hanya a nan kenan.
Akwai nau’in ababen da mace za ta rika ci, sannu a hankali, kyan diri da halittarta za su kara fitowa, ita ma za ta rika ji ta kara cika, ta yi kyau.
Masana a fannin sanin abinci mai gina jiki sun bayar da shawarwarin amfani da:
– Madarar ruwa
– Zuma
– Abarba
– Ayaba
– Kankana
– Gwanda
Yadda Za’a Hada Shine Kamar Haka:
A kan hada su waje guda, a markada su, har sai sun zama ruwa,sai a dan kara zuma da madara. Bayan wannan,mace za ta rika sha a koda yaushe. Haka kuma kina iya samun Zogale dafaffe, ki hada da ganyen Alayahu, ki zuba Tumatiri da Albasa, ki yi kwadonsu, ki rika ci.
Haka nan za ki rika yin wadannan kayan lambun da ki ka markada, sai ki rika sha misali da asuba ko da sassafe kafin ki fara cin komai.
Allah yasamudace yarufamana asiri Ameen Ameen 🤲🤲🤲