.
🏥 Magunguna

Jerin cututtukan cikin Farjin Mace da hanyoyin magance su cikin sauki

Jerin cututtukan cikin Farjin Mace da hanyoyin magance su cikin sauki

Jerin cututtukan cikin Farjin Mace da hanyoyin magance su cikin sauki

Kusan dukkanin abinda yake kawowa mata jinya ko kuma cututtuka a cikin farjin su yana da kyakkyawar alaka da amfani da sukeyi da ruwan sanyi wajen aiwatar da hidimomi da bukatu na yau da kullum, kamar yin tsarki da ruwan sanyi ko kuma yawan yin wanka dashi.

To dai ana bukatar mace ta gujewa yawan amfani da ruwan sanyi saboda illa ce a gare ta.

Ko da yaushe ana bukatar mace ta kasance mai amfani da ruwan dumi wajen tsarkin fitsari, da kashi, da haila (al’adar), da tsarkin jinin biki, sannan a cikin ruwan dumin a dan kada alumu kadan kadan a ciki.

Haka zalika idan mace tana fama da wasu ko kuma duka daga cikin wadannan abubuwa masu barazana ga lafiyar su kamar;
– Warin farji
– Fitar farin ruwa a cikin farji
– Kuraje farji
– Karnin farji
– Kumburin farji
– Kaikayin farji.
– Ko kina jin wani abu yana miki yawo a cikin farjinki ko kuma datti ya shiga, sannan kin barshi har ya dankare kin rasa yadda zakiyi dashi…..subhanallah.

Babban abinda ya kamata kiyi shine neman magani wanda zai kore miki wannan damuwa, domin lafiyar ki ita ce alfaharin ki wajen mijin ki.

To maganin wadannan cututtuka da kuma yadda za’a hada su, sune kamar haka :

Zaki sami ganyen magarya, ki wanke shi ki sashi a tukunya cike da ruwa, ki tafasa shi sosai, sai ki dauko shi daga kan wutar a barshi shi ya huce.

Sai kina wanke farjinki dashi, sannan ki dan debi kadan kina sha, sannan zaki iya samun roba mai fadi ki zuba shi a ciki kina shiga cikin robar tsawon minti 30. Haka zalika a samu man zogale a dinga sha kamar cokali biyu da rana, biyu da daddare.

Idan kinason haɗa zumar mata akwai kayan haɗi na musamman da zaki nema kamar haka ;

1 ‘Yayan minna nas
2 Kanunfari
3 Bawon kabewa
4 Bawon kokumba
5 Bawon kankana
6 Zuma

Bayanin yadda za’a haɗa;

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki dakesu su zama gari ki dunga sha da zuma, hmmmm yar uwa zaki san kin sha hadin zumar mata.

Allah yasa mudace.  Ameen summa Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button