Hanyar da zaki gyara Nononki su ciko sannan su tashi tsaye
Hanyar da zaki gyara Nononki su ciko sannan su tashi tsaye

Hanyar da zaki gyara Nononki su ciko sannan su tashi tsaye
Dukkanin macen da tasan hanyar yadda zata gyara nononta to tabbas ta kama hanyar cika macen da maza za suna tururuwa akanta. Saboda a dukkan jikin mace, nonon ta shine lamba na biyu dake bayyana kyawunta, sannan lamba na daya da yake bayyana cikar surar ta.
Idan dai kuwa hakane, babban abinda ya kamace ku mata shine, ku jajirce da gyara da kuma kula da shi domin jan hankalin maza da yawa a kanku.
Maza da yawa suna son suga kirjin mace ya ciko ya tsaya yayi kyau ko babu komai akwai kyawon gani,wasu kuma basu damu da wannan ba amma da yawa maza suna son sa sosai domin yana da nashi rawar da yake takawa a wajen kwanciya yayin wasanni.
Sannan yan mata da yawa suna samun kalubale daga samari idan suna da kananan halitta na Nono,wasu kuma da auren nasu amma sun bari ya zube ya lalace ya zama babu kyawun gani.
Wata haihuwar bata wuce daya ko biyu na amma idan ka ganta tambayar wata uwar marayu duk ta bari sun zube sun lalace.
Ga hanyar da zaa bi domin gyarwa tare da kara musu kyawun gani.
ABINDA ZAA NEMA:
– Garin plantain (Filenten) gwangwani 2 da rabi
– Garin hulba gwangwani 1
– Shinkafar tuwo gwangwani 1
– Gyada rabin gwangwani
Yadda Za’a Hada:
Dukkan su za’a hade su waje daya a dake su sosai sannan a rika yin salala (kunu) dashi a rika sha da safe kafin a karya zuwa tsawon wata daya.
Insha Allah wannan hadin bayan gyaran nono da yake har gyara jiki yake da karin kiba da kuma sauran bangare na gyaran jiki.
Allah yasa mudace.