Hanyar da zaka hada ingantaccen maganin jimawa kana saduwa da iyalin ka
Hanyar da zaka hada ingantaccen maganin jimawa kana saduwa da iyalin ka

Hanyar da zaka hada ingantaccen maganin jimawa kana saduwa da iyalin ka
Wanda yake ganin lokacin da yake jima’i yayi masa kadan saboda ko kuma sakamakon wata lalura da yake fama da ita, to yau yayi gamo da mafitar sa bisa yardar ubangiji. Namiji yana son ya burge mace ta hamyoyi da dama wanda jimawa ana jima’i shi ma yana daga ciki.
Amma a lokacin daka fuskanci cewa kana da raunin al’aura wato azzakarin ka baya mikewa ko kuma baya daukar lokaci yana aiki kamar yadda ya kamata, to ba tsayawa za kayi kana tunani ba, neman magani za kayi.
Indai kana Namiji baka iya gamsar sa iyalin ka lallai kana sa babbar Matsala wacce yana da kyau kuma ace ka magance ta domin gudun samun matsala tsakanin ka da iyalin ka, wannan ita ce maganar gaskiya.
Don haka ga wata hanya mai sauki domin samun waraka akan wannan lamari domin a gamsar da iyali a sauke musu hakkin su wanda ta haka ne za’a samu a zauna lafiya.
Abubuwan hadin kuwa sune.
– Zuma
– Lemon tsami
– Na’a Na’a
Yadda za’a hada su shine.
Za’a samu Na’a Na’a kamar kunne 20 sai a wanke sosai a zuba mata ruwa kofi 1 a matsa lemon tsami guda daya a matsa a saka bawon a ciki a tafasa sosai,bayan an sauki a barshi ya wuce sai a zuba Zuma chokali 2 a ciki.
Yadda za’a hada ingantaccen maganin karfin maza ga wadanda suke da lalura ta raunin mazakuta
Raunin azzakari yana daga cikin abubuwan da suke damun maza da yawa a lokacin da suke son biyawa kansu tare da iyalin su bukata wajen yin jima’i. To babban abinda ya kamata mutum yayi shine ya kokartawa kansa don binciko mafita ta waraka ga kansa da kuma jindadin mai dakin sa.
Ingantaccen karfin Maza ma’ana mazakuta yana da matukar muhummanci ga rayuwar maza musamman bangaren zamantakewar iyali, domin sautari maza kan samu matsala wajen biyawa iyalansu bukata saboda irin wadannan matsalar da suke fama da ita, wadda a karshema wata macen saki zata nema kai tsaye daga wajen abokin rayuwarta saboda wannan damuwar.
Insha Allahu wannan magani da zamu bayar a kasa ba iya karin karfin mazakutar yake ba, haka zai karawa mazakutarka Girma, Karfi wajen Jure Jima’i mai tsawo, da kuma magance matsalar sanyi ko wanne iri ne insha Allahu.
Abubuwan Da Yakamata A Nema Domin Hada Wannan Maganin Sune :
Tafarnuwa
Citta
Kununfari
Zuma
Albasa
Ga Yadda Zaku Hada Maganin Cikin Sauki ;
Za’a samu albasa mai kyau sai a nikata sosai tazama ruwa. Sannan a kawo tafarnuwa sai a nikata, amma ruwan nikan tafarnuwar yazama dan kadan.
Cittakar kuwa da Kanunfari ana dakasu sosai suyi laushi.
Bayan ka gama da wadannan abubuwa saika samo kofi da cokali saika debi kamar cokali biyu na Albasa, cokali biyu na Tafarnuwa, cokali biyu na Kanunfari da kuma cokali biyu na Citta, akarshe saika debi cokali kamar Hudu na Zuma saika hadasu gaba daya a kofin nan saika juya sosai kashanye duka.
Wannan hadi a rana sau biyu kawai za’ayi, kuma insha Allahu za’a samu kyakyawan sakamako.
Allah yasa mudace.