.
📻 Labaran Hausa

Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

Murja Kunya: An Koma Kotu Yau , Alkali Ya Ce A Cigaba da Tsareta a Kurkuku

 

A yau Alhamis, 16 ga watan Febrairu, shahrarriyar yar dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta sake gurfana gaban kotun shari’ar Musulunci dake Filin Hoki jihar Kano, Arewa maso yammacin Najeriya.

 

Arewa Radio ta ruwaito cewa Alkali Mai Shari’a yayi umarni a maida Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali da tarbiyar zuwa mako guda.

 

Murja dai har ila yau ta musanta tuhumar da ake yi mata a gaban kotu.

 

Freedom Radio ta ruwaito cewa game da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba.

 

Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Yiwa Yan Najeriya Jawabi a Ranar Alhamis

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa ‘yan Najeriya kan halin da ake ciki a kasar nan da kuma mafita.

 

Ana kyautata zaton jawabin zai mai da hankali ne ga yadda karancin sabbin Naira ke shafar rayuwar ‘yan Najeriya.

 

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale tun bayan kaddamar da sabbin kudi a kasar a shekarar da ta gabata.

 

FCT, Abuja – A ranar Alhamis da misalin karfe 7 na sanyin safiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yiwa ‘yan kasa jawabi, The Nation ta ruwaito.

 

Wannan na fitowa ne daga bakin mai ba shugaban kasa shawari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina a cikin wata sanarwar da ya fitar.

 

Adesina ya bayyana cewa, za a yada jawabin shugaban kasan a gidajen talabiji, rediyo da sauran kafafen yada labarai na kasar.

 

Ya zuwa yanzu dai ba san dalilin da yasa shugaban kasan zai yiwa ‘yan Najeriya jawabi ba a daidai lokacin da ‘yan kasar ke cikin matsi.

 

Jawabin na shugaban kasa dai na zuwa ne daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kuka kan yadda karancin takardun Naira ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button