Kotun Koli Ta Dage Shari’ar CBN da Gwamnonin Najeriya 12 Kan Batun Fasalin Kudizuwa 22 Ga Fabrairu
Kotun Koli Ta Dage Shari’ar CBN da Gwamnonin Najeriya 12 Kan Batun Fasalin Kudizuwa 22 Ga Fabrairu

Kotun Koli Ta Dage Shari’ar CBN da Gwamnonin Najeriya 12 Kan Batun Fasalin Kudizuwa 22 Ga Fabrairu
Kotun koli a Najeriya ta dage karar da aka shigar gabanta kan kudurin CBN ta tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin kudi a kasar.
Babban Bankin Najeriya ya sauya fasalin N200, N500 da N1000, ya ce daga ranar 10 ga watan Faburairu tsoffi sun daina aiki, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na Kogi da Bello Matawalle na jihar Zamfara sun ce ba za ta sabu ba, sun kai kara kotu.
A zaman ta na baya, kotun ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudi har zuwa ranar 15 ga wata, wato yau kenan don ya sake sauraran karar.
Jihohi da yawa a kasar nan sun nuna sha’awar shiga jerin wadanda ke kalubalantar gwamnatin, inda suka amince da ra’ayin jihohin uku na sama.
A zaman na yau, mai shari’a John Okoro ne ya jagoranci alkalai bakwai na kotun koli don sake sauraran karar.
Ya ce, kotun ba za ta yi biris da karar ba da manufarta kasancewar ta shafi yadda ‘yan kasa ke shan wahala.
Tuni alkalan suka amince da shigar da karin jihohi tara da ke sha’awar shiga shari’ar, kuma ya dage ci gaba da zama zuwa 22 ga watan Faburairu 2023.
Karin bayani na nan tafe.