
GA AMFANI 9 DA GYADA KEYI A JIKIN MUTUM:
🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜🥜
1.🥜 Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawan zuciya.
2🥜. Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.
3.🥜 Yana dauke da sinadarin ‘Phylosterols wanda ke kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
4🥜. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar siga.
5🥜. Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.
6🥜. Gyada na kara karfi a jiki.
7🥜. Yana bunkasa girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.
8🥜. Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda akawai sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.
9🥜. Gyada na faranta wa mutum rai musamman masu yawan fushi.
Ita kunne kanta an kasa shi bari uku (3) :
1- Outer ear = wajen kunne .
2- Middle ear – Tsakiyar kunne
3- Inna ear – Cikin kunne .
Mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining ciwon tsakiyar kunne ne ( Otitis media ) .
ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE :
Yana daga cikin abubuwanda suke kawo ciwon tsakiyar kunne :
1- kwayar cututtuka kamar su :
a- bakteria
b- virus
Amma mafi yawa bakteriya ne , wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. ( akoi hanyar da tahadasu dama).
2- Anasamun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu kamar Burbushin Kura , Gashin magye da sauransu ( Allergies).
HALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE :
1- Mutun zaiji kamar wani abu ya cika masa kunne .
2- Rashin ji sosai
3- Zubar da ruwa a kunne
4- Jin zafi a cikin kunne .
5- kaikayin
6- Zazzabi da ciwon kai .
MENENE ALAKAR MURA DA CIWON KUNNE :
Gaskiya akoi alaka tsakanin mura da ciwon kunne , mafi yawan mura yana kama hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akoi hanyar da tahada tsakanin Makogoro da Hanci dakuma tsakiyar kunne .
Kamar yadda mukace kwayoyin cutar bakteriya , da virus da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne.
To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro , hanci da kunne.
SHIN DIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANI CIWON KUNNE :
Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su gentamycin bai kamata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.
Dalili shine wani lokocin ana samun fujewan dodon kunne (rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.
MAGANIN CIWON KUNNE :
Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya takawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment , hakanan wanda aka samu da dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.
GARGADI
Diyawa daga cikin mutane idan kunnensu yana ciwo kawai zuwa suke chemist a wanke musu kunne.
Bincike ya nuna akoi sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana wasu kwayoyin cuta na bakteriya da makamantansu girma da shiga cikin kunne, a garin wanke daudan kunne idan aka wanke wadannan sinadaran to daga nan anbudewa kwayoyin cuta kofa ne .
WASSU ZA KAGA SUNA YAWAN KWAKULE KUNNE:
Amfanin “dauɗar kunne” da illar ƙwaƙwale ta.
“Dauɗar kunne” wani ruwa ne mai ɗan danko da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saɓanin yadda Bahaushe ke cewa “dauɗar kunne” ce . Saboda haka “dauɗar kunne” ba dauɗar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje.
Allah da ikonsa, kamar yadda kunne ne ke samar da wannan “dauɗar kunne”, haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan “dauɗa” da kansa.
Daga cikin amfanin “dauɗar kunne” akwai:
1. Cafke dukkan nau’in ƙura, ƙasa, ƙwari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.
2. Kashe kwayoyin bakteriya, da sauransu.
Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:
1. Magogin kunne wato ‘cotton bud’ a turance.
2. Tsinken tsintsiya
3. Mirfin biro
4. Kan ashana
5. Gashin kaza, da makamantansu.
Sanya waɗannan abubuwa cikin kunne don ƙwaƙwalo “dauɗar kunne” na da haɗarin:
1. Ƙara cusa “dauɗar” zuwa can cikin kunne.
2. Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.
3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.
4. Raunata gangan kunne yayin da irin waɗannan abubuwa suka zarme cikin kunne.
5. Shafe ko manne “dauɗar kunnen” a kwararon kunne.
Haka nan, zira waɗannan abubuwa cikin kunne don susa ko ƙwaƙwalo “dauɗar” akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share ƙwararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baƙin abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.
Kada ka ɗauki ɗabi’ar sa magogin kunne cikin kunne don goge “dauɗar kunne” kullum.
Tuntuɓi likitan kunne da zarar ka fara jin wani ɓaƙon yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga “dauɗar kunnen”.
Lafiya Uwar Jiki
AMFANIN YIN JIMA’I AKAI-AKAI GA MACE MAI CIKI
Ba kamar yadda wasu ke tunani ba. Jima’i da mace mai dauke da juna biyu yanada mahimmanci ga ita mai ciki cewar masana.
Ga wasu alfanun da masana suka kawo su ga macen da ake Jima’i da ita idan tana da ciki.
1:Yakan Sa Haihuwa Cikin Sauki: Masana sukace macen da ake yawaita kwanciyar aure da ita bayan ta samu ciki, zata haihu cikin sauki ba tare da doguwar nakuda ba.
Wannan yasa suka baiwa ma’aurata shawaran cewa, kada su sausautawa Jima’i koda kuwa gobe ne macen ake saran zata haihu.
2: Samun Bacci: Jima’i da mace mai ciki yakan sata ta samu bacci mai dadi a duk lokacinda aka sadu da ita.
Ana kammala saduwa da mace mai ciki zata samu wani bacci mai dadin gaske da zata manta duniyar datake ciki.
Don haka ma’aurata kada suyi kasa a gwaiwa wajen Jima’i da ciki.
3: Yana Warware Gajiya: Duk irin gajiya ko damuwa da mace mai ciki take da shi ana saduwa da ita zata ji watsai inji masana.
Wannan yasa duk wata mace mai ciki yana dace a yi Jima’i da ita a lokacinda jikinta yayi laushi ko kuma ta shiga wata damuwa.
4: Narkar Da Kitsai: Masana sukace duk mace mai ciki da ake yawan saduwa da ita kitsai ba zai taru mata a jikinta ba.
Kowa dai yasan illar da kitsai yake dashi a jikin mutum. Amma ita mace mai ciki ta hanyar Jima’i zata samu waraka matsalar kitsai a jikinta.
5: Maganin Hawan Jini: Duk wata mace mai ciki akwai yiwuwar ta kamu da cutar hawan jini. Amma idan har tana baiwa mijinta gabanta akai akai da cikin, bazata samu wannan matsalar na hawan jini ba inji masana.
Wadannan sune wasu daga cikin alfahun yin Jima’i da mace mai juna biyu kamar yadda likitoci suka tabbatar.
Sai dai kuma yana da kyau maza su fahimta, akwai wasu matan da kwata kwata basa son yin Jima’i idan suna da ciki, idan matarka tana cikin irin wadannan matan, kada ka takura kace dole sai kunyi. Kawai idan tana sha’awar yin Jima’i da ciki to kada ka saurara mata domin samun lafiyanta ne hakan. Idan kuma bata so, sai kayi hakuri.