CBN Ya Ce Zai Kama Duk Mai POS da Ke Karbar Sama da N200 WajenCire Kudi
Gwamnan CBN ya bayyana cewa, za a dauki mataki kan masu POS da ke karbar caji fiye da kima a Najeriya.
Ya ce babu bukatar kara wa’adin da ya dauka na daina amfani da tsoffin kudade a fadin kasar nan.
Asusun ba da lamuni na duniya ya shawarci CBN da ya dage wa’adinsa domin ba ‘yan kasa damar shigar da kudadensu.
FCT, Abuja – Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya ce, dukkan masu hada-hadar kudi na POS da aka kama suna karbar cajin cire kudi sama da N200 za su fuskanci hukuncin jefa su a magarkama.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar barazanar karancin sabbin Naira a bankuna da hannun ‘yan POS, Punch ta ruwaito.
Idan baku manta ba, CBN ya nada wakilai daga bankuna da ‘yan POS domin taimakawa wajen musayar kudade a fadin kasar nan.
Da yake magana a ranar Talata yayin da ya ziyarci ministan harkokin wajen kasa, gwamnan CBN ya yi batutuwa kan sabbin ka’idoji da dokokin kudi na CBN.
A cewarsa
“Lamarin a hankali ya fara lafawa tunda aka kawo tsarin ba da kudi a kan kanta don tagazawa cire kudi ta ATM da kuma a hannun agent-agent dinmu.
“Don haka, babu bukatar sake matsar da wa’adin na ranar 10 ga watan Faburairu.”
Batun umarnin kotun koli
Idan baku manta ba, rahotanni a baya sun bayyana yadda kotun koli ya ba da umarnin a ci gaba da karbar tsoffin kudi har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu.
Kotun ya ce, zai sake zama a ranar 15 ga watan domin duba yiwuwar tursasa CBN wajen tabbatar da an ci gaba da karbar tsoffin kudi, rahoton Vanguard.
Har ila yau, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya shawarci CBN a makon da ya gabata kan ya kara wa’adinsa na 10 ga wata don ba ‘yan Najeriya damar shigar da tsoffin kudi.