.
📻 Labaran Hausa

Saudi ta Bankara Doka Saboda Cristiano Ronaldo Ya Zauna Tare da Budurwa Babu Aure

Saudi ta Bankara Doka Saboda Cristiano Ronaldo Ya Zauna Tare da Budurwa Babu Aure

Saudi ta Bankara Doka Saboda Cristiano Ronaldo Ya Zauna Tare da Budurwa Babu Aure

 

Saudi Arabiya tana cikin Kasashen da ke kokarin kamanta bin shari’ar addinin Musulunci a Duniya.

 

Wannan ya sa dokar Gwamnatin Suadiyya ba ta bari mutane su zauna tare alhali ba su auri juna ba.

 

Dokar ta sha bam-bam a kan Cristiano Ronaldo wanda yake rayuwa tare da Georgina Rodriguez.

 

Saudi – Tsohon ‘dan wasan kungiyoyin kwallon kafa na Manchester United da Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya shiga sabuwar rayuwa a Saudi Arabiya.

ES Sport ta rahoto cewa akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya yi sallama da kwallon kafa a Turai har abada, domin ya yi sallama da dillalinsa, Jorge Mendes.

 

Cristiano Ronaldo zai koma rayuwa a Saudi Arabiya bayan ya koma taka leda a Al Nassr a dalilin datse kwantiraginsa da kungiyar Manchester United tayi.

 

Sai dai Ronaldo yana rayuwa ne tare da budurwarsa kuma uwar wasu daga cikin ‘ya ‘yansa watau Georgina Rodriguez mai shekara 28 duk da ba su yi aure ba.

 

A dokar Saudiyya, bai halatta mace da namiji su zauna a karkashin rufi daya ba tare da aure ba. Ko da Ronaldo ya dade tare da Rodriguez, bai aure ta ba tukun.

 

Rahoton ya bayyana cewa wannan dangataka za ta zama banbarakwai a wajen mutanen Saudi.

 

Abin da Lauyoyi suke fada a kan dokar

 

Wani Lauya ya bayyana cewa duk da doka ba ta amince a zauna a gida daya ba tare da yin aure ba, mahukuntan Saudi sun fara nuna ko-in-kula kan wannan.

 

Masanin shari’an yake cewa an fi tunawa da dokar idan har an samu wata matsala, ko ana zargin mutum ya aikata wani laifi, sai a fara kokarin hukunta shi.

 

A cewar wani lauyan na dabam, wanda shi ma bai bari an kama sunansa ba, gwamnatin Saudiyya ba ta cika damuwa da rayuwar bakin da suka shigo ba.

 

Amma duk da haka, Lauyan ya ce bai halatta ‘yan kasar su tare idan babu igiyar aure a tsakaninsu ba. Wata jaridar kasar Sifen ta fitar da rahoton nan a makon nan.

Georgina Rodriguez da Ronaldo

 

Kwanaki kun samu rahoto cewa a duk wata, Ronaldo ya na ba Georgina Rodriguez kimanin €100,000 domin ta rika dawainiya da gida da kuma ‘ya ‘yansa.

 

Georgina Rodriguez ta haifi wasu daga cikin ‘ya ‘yan Ronaldo, daga ciki har da tagwaye a watannin baya, daga cikinsu ne akwai daya bai zo da rai ba.

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button