.
🏥 Magunguna

KALOLIN ABINCIN 10 DAKE KARAWA

KALOLIN ABINCIN 10 DAKE KARAWA

Domin karawa kan ku sha’awa da biyawa matanku bukata lokacin saduwa sai kuyi amfani wadannan abubuwa guda 10

KALOLIN ABINCIN 10 DAKE KARAWA NAMIJI SHA’AWA WURIN JIMA’i.

Gargadi: Duk Wanda bashi da aure ya
rage cin su kuma, domin yana tada sha’awa, idan ka tabbatar zaka yi jima’i zakana cin wadannan abubuwan da zamu lissafa muku domin zasu taimaka muku.

(1) Ridi: Ta yiwu ka yi mamakin an ambaci ridi, to ba abin mamaki game da haka domin kuwa masana sun tabbatar da cewa yana kunshe da sanadarai na zinc dake habaka yawan maniyyi ga namiji, wanda hakan ke kara masa
sha’awa.

(2) Kankana: Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2008 ya nuna yadda kankana ke kara kuzari ga namiji, saboda wasu muhimman sanadaran da take kunshe da su, harma wasu sukan misalta ta da irin magungunan jima’i da wasu ke sha.

(3) Barkono wato Yaji: Wasu basu san dangantakar gudanuwar jini a jikin dan adam da jima’i ba, yadda al’amarin
yake yayin da sha’awar mutum ta motsa,
hanyoyin jini dake jikin al’aurarsa sukan bude sai jini ya kwarara, hakan yake sanya al’aurar tasa yin karfi har ya samu damar gabatar da jimai ba tare da matsala ba.

To shi barkono yana da sinadaran da suke aiwatar da irin wannan aiki a jikin dan-adam.

Amma ba ana nufin mutum ya debi yaji ya
sha ba a’a zai hada shine da abinci, haka
nan kuma ana fadakar da mutane wajen
takaita amfani da shi musamman ga
wadanda idan sun ci da yawa zai haifar musu da wata matsalar.

(4) Citta: Ita ma citta tana aiki ne kwatankwacin nayaji kamar yadda yaji ke taimakawa wajen kwararar jini zuwa ga al’aura namiji, haka ita mata ke yi.

Sai dai kari akan na barkono ita tana kara lafiyar hanyoyin jinin.

(5) ‘Yayan kabewa: Ba shakka ‘yayan kabewa na kunshe da sanadarai ne dake kara sha’awa da kuma kuzariga namiji.

(6) Ayaba: Masana sun gano cewa ita ayaba tana kunshe da sinadarin potassium, hakan yasa masanan suka bayyana yadda take karawa namiji kuzari, musamman idan yaci mintuna 30 kafin saduwa da iyali.

(7) Dankali: Dankali ko na gargajiya ko na turawa shima yana kunshe da sinadari potassium dake inganta karfin mazakutar namiji, hakan kuma na inganta saduwa tsakanin ma’aurata.

(8) Gyada: Ita kuwa gyada wani sinadari take kunshe da shi da ake kiran sa amino acid L-arginine da turanci, shi wannan sinadari na taimakawa wajen dadewar gaban namiji a mike.

9.Tafarnuwa: Shekaru dubbai da suka shude mutanen kasar masar ke amfani da tafarnuwa don gudanar da magungunan matsalolin jiki daban daban.

Har ya zuwa wannan zamani da masana suka gudanar da bincike na zamani don tabbatar da irin alfanunta ga lafiyar dan adam.

Binciken zamanin ya tabbatar da cewa, ita tafarnuwa na gyara hanyoyin jini kuma mun bayyana a sama yadda gudanuwar jini ke da alaka da mikewar gaban namiji.

Hakanan tana gyara zuciya wadda itama an san aikinta na wajen tunkuda jini cikin jiki, don haka wannan na bayuwa zuwa ga karfin al’aura yayin jima’i.

(10) Kwai: Ba sai an fada ba mun san kwai na kunshe da sinadarai masu gina jiki game da jima’i kuwa akwai sinadaran B6 da B5.

Bincike ya nuna wadannan sinadarai suna kawar da damuwa su kuma inganta sha’awar jima’i ga namiji.

Allah yasa mudace Ameen Ameen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button