.
📻 Labaran Hausa

Babu hannu na wajen ficewar Nafisa Abdullahi daga cikin shirin Labarina wallahi – Nuhu Abdullahi

Babu hannu na wajen ficewar Nafisa Abdullahi daga cikin shirin Labarina wallahi – Nuhu Abdullahi

Babu hannu na wajen ficewar Nafisa Abdullahi daga cikin shirin Labarina wallahi – Nuhu Abdullahi

 

Nuhu Abdullahi Yayi Martani Ga Masu Cewa Shi Ya Ingiza Nafisa Abdullahi Ta Fita Daga Shirin Labarina, Jatumin Yayi Bayani. Jarumi Nuhu Abdullahi Wato Mahmud A Cikin Shirin Labarina.

 

Yayi Bayani Game Da Mutanen Dake Cewa Shiya Ziga Nafisa Itama Ta Fita Daga Shirin Labarina Series.

 

Jarumin Ya Sami Bada Amsar Ne A Kujerar Gabon Talk Show, Inda Ya Halarci Shirye Shiryen Da Hadiza Gabon Ke Gabatarwa.

 

Hadiza Gabon Din Tayiwa Nuhu Abdullahi Tambayoyi Da Dama, Inda Shima Ya Bata Amsa Dai Dai Irin Tambayoyin Data Mishi.

 

Idan Baku Manta Ba, Kusan Lokaci Guda Akaga Nafisa Abdullahi (Sumayya) Tare Da Nuhu Abdullahi (Mahmud) Su Yanke Alakarsu Da Kamfanin Saira Movies, Inda Hakan Yasa Su Futa Daga Cikin Shirin Na Labarina, Fitasu Daga Shirin Yasa Mutane Su Dinga Cece Ku Ce.

 

Kan Cewa Ana Ganin Kamar Nuhu Abdullahi Shi Ya Hurewa Nafisa Abdullahi Kunne Domin Itama Ta Fita Daga Shirin Bayan Shi Ya Fara Ficewa.

Ga cikakkan video 👇👇👇👇

 

 

A wani labarin kuma

An ɗaura Na zama matar Abba, Allah Nagode maka, Bidiyon amarya cike da farinciki mara misaltuwa

Wani bidiyo ya yi matukar daukar hankalin mutanen shoshiyal midiya bayan ganin wata amarya cike da farinciki mara misaltu

 

A bidiyon wanda take sanye da kaya launin farare da alamu ranar aurenta ne ya dauki hankali, shafin Gaskiya zalla na Instagram ya wallafa.

 

A bidiyon an ga yadda ta kasa boye farincikinta inda ta kwashi rawa tana daga hannunta sama tana godiya ga Ubangijin da ya nuna mata ranar aurenta.

 

Ko da gani tana matukar kaunar angon nata mai suna Abba wanda hakan yasa ta kasa boye murnar. An ji tana cewa:

 

“An daura an daura, na zama matar Abba. Allah Nagode maka.”

 

Martanin Mutane

@hajjasalmacollectionlagos:

Dan Allah anemomana abba mugansa

@xeedamulky :

@hajjasalmacollectionlagos wlhy nima zan so naganshi

@beentuameen cewa take

MashaAllah Allah ya dauwamar muku da farinciki.

 

Wannan bidiyon ya dauki hankali sosai. Wasu na ganin rashin kunya ne tayi. Inda wasu kuma ke ganin tsabar siyayyar da ke tsakaninta da angonta ne ya janyo hakan.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button