.
📻 Labaran Hausa

Babban Likita A Ekiti ya mutu yana gwada kwazonsa da matar fasto a otel

Babban Likita A Ekiti ya mutu yana gwada kwazonsa da matar fasto a otel

Babban Likita A Ekiti ya mutu yana gwada kwazonsa da matar fasto a otel

Wata majiya ta ce likitan dan kasar ya mutu ne sakamakon jima’i da matar wani Fasto.

Shahararren likita a jihar Ekiti ya mutu sakamakon zargin yin lalata da matar wani Fasto a wani gidan otel a jihar.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a Ikere Ekiti. Kamar yadda jaridarmikiya na ruwaito.

Majiyoyi a garin sun bayyana cewa marigayin mai suna Kehinde ya sauka ne a daya daga cikin dakunan otal din tare da matar.

Wata majiya, wadda ba ta son a buga sunanta, ta shaida wa jaridar The Gazette cewa matar faston ta tayar da hankali game da lamarin lokacin da ta fice daga dakin.

Mutumin ya mutu ne a cikin dakin bayan da ya yi jima’i da matar.

“Matar ce ta buga kararrawa bayan ta fahimci cewa ya fadi. Sai da manajan ya garzaya ya kai mutumin asibiti da ke kusa, amma abin takaici da isowar sa ya mutu,” inji majiyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata, inda ya kara da cewa an fara gudanar da bincike kan lamarin.

Mista Abutu ya ce matar da ta riga ta kasance a hannun ‘yan sanda, za ta rika taimaka wa jami’an tsaro wajen bankado al’amuran da suka haddasa mutuwar Likitan.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, “an dauko gawarsa an ajiye shi a dakin ajiyar gawa”.

A wani labarin kuma

Kotu ta raba auren da kaka ya yi da jikarsa tsawon shekaru 23

Wata babbar kotun shari’ar musulinci da ke zaman ta a Tsafe dake Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a jiya Talatar nan ta raba auren wani mutum mai suna Musa Tsafe da jikarsa Wasila da suka shafe shekaru 23 da yin aure.Shafin Daily Nigerian Hausa na ruwaito

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, Malam Bashir Mahe, ya raba auren ne bayan sauraren karar daga bangaren masu gabatar da kara da kuma lauyoyin masu kara.

Mahe ya ce auren Musa da Wasila ya saɓa wa koyarwar Addinin Musulunci.

Alƙalin ya ce auren da ke tsakanin ma’auratan ya saba wa Alkur’ani kamar yadda yazo a sura ta 3 aya ta 23, shafi na 79 da shafi na 77 na hukunce-hukunce.

Ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan gazawar lauyan da ke kare wanda ake tuhuma.

Hukumar Hisbah ta shigar da kara ne inda take neman a raba auren na tsawon shekaru 23.

Hukumar ta shaida wa kotun cewa auren Musa da Wasila ya saba wa tsarin shari’ar Musulunci.

Hukumar ta ce ta tilasta shigar da kara a kan ma’auratan ne bayan kokarin da Majalisar Shawarar Musulunci (Shura) da Masarautar Tsafe suka yi tun a shekarar 2020 bai haifar da da mai ido ba.

Lauyan hukumar Malam Sani Muhammed ya shaidawa kotun cewa binciken da hukumomin addinin musulunci daban-daban da masarautar suka gudanar ya nuna cewa ma’auratan da suka yi aure tun wani lokaci a shekarar 1999 suna da alaka kai tsaye don haka an haramta aure a tsakaninsu.

Muhammed ya ce matakin ya sabawa koyarwar Addinin Musulunci kamar yadda aka yi nuni a cikin Alkur’ani sura ta uku aya ta 23.

Don haka ya roki kotu da ta gaggauta raba auren.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya ruwaito cewa Musa Tsafe, yana da ‘ya’ya takwas tare da matarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button