.
Education

Labarina wasu mata su,uku dasukayi abin al,ajabi turanci da hausa, My story is about some women, three of them have a wonderful English and Hausa language

Labarina wasu mata su,uku dasukayi abin al,ajabi turanci da hausa, My story is about some women, three of them have a wonderful English and Hausa language

Labarina wasu mata su,uku dasukayi abin al,ajabi turanci da hausa,

My story is about some women, three of them have a wonderful English and Hausa language

 

Once upon a time,
Can awani alokaci,

there were three sisters,
anyi wasu ‘yan uwa mata su uku,

the two older ones envied their younger sister for her beauty,
Sai manyan biyu suka rinka yiwa karamar tasu hassada saboda kyawun ta,

and for extra love their mother lavished upon her.
da kuma irin fifikon soyayya da uwar su ta dora mata.

When the mother died she left each one her own inheritance:
Lokacin da uwar ta rasu ta barwa kowace daya gadon ta:

the older one got her mother’s palace and guards
babbar ta samu Fadar uwar ta da masu hidima,

the middle one got her mother’s jewels and money,
ta tsakiyar ta samu lu’u-lu’un uwarta da kuma kudi,

and the youngest one got only an old book.
karamar su kuma ta samu wani tsohon littafi ne kadai.

The good girl was very satisfied with her inheritance,
Yarinyar kirki sai ta gamsu da nata gadon,

she cherished the book and she took good care of it keeping it stashed away in her closet for years.
Sai ta so shi ta kula dashi ta kuma adana shi a cikin kabod din ta na tsawon shekaru.

 

Anxiously the two sisters watched her, for they could never believe that their mother would favour them to her pampered daughter.
Cikin zulumi sai ‘yan uwan biyu suka samata ido don bazasu iya amincewa ba cewa uwar su zatayi musu gatan da yafi na’yar lelenta ba.

When the girl grew older she got her mother’s gift out of the closet one day cherishing her mother’s memory,
da yarinyar ta girma sai ta fito da kyautar da uwar tayi mata wata rana daga kabod tana murnar tunawa da uwar ta.

and she started to cry for she really missed her.
Sai ta kama kuka saboda ta rasa ta.

She suddenly noticed that the book was double bound,
Sai ta gano ashe littafin ma dauri biyu ne,

and when she pushed up the outer binding,
Lokacin da ta tura daurin farko,

seven long hairs fell on her lap along with a small folded paper.
Sai dogayen gashi guda bakwai suka fado kan cinyar ta tare da wata nadaddiyar takarda.

She opened the folded paper and read what was written on it.
Sai ta bude nadaddiyar takarda ta karanta abinda ke ciki.

Here are seven hairs, every time you need to see me,
Ga gashi nan guda bakwai duk lokacin da kika so gani na,

burn up one and I will come for you.
Sai ki kona guda daya zan zo miki.

At the night the girl burned the first hair
Da dare yayi sai yarinyar ta kona gashin farko,

Suddenly the young man appeared out of no where.
Nan take sai wani saurayi ya bayyana agareta wanda ba asan daga inda yake ba,

and he was so beautiful he could easily be deputy of the moon.
yanada kyawu sosai, lallai tana yiwuwa kila ma mataimakin wata ne.

He spoke to her saying: Peace be upon you.
Sai yayi mata magana yana cewa: Amincin Allah ya tabbata agareki.

 

 

 

My name is Sprig of elixir you called me up,
Suna na fulawar ruwan rayuwa kin kira ni,

and this is the bag of gold a gift from me to you.
ga jakar zinare kyauta ce daga gareni zuwa gareki.

When her sisters asked her in the morning where she got the gold,
Lokacin da ‘yan uwanta suka tambayeta da safe ina ta samo zinare,

She was hesitant to tell them for a while,
Tayi dari-darin fada musu na wani dan lokaci,

but then they kept poking her until she recounted the whole incredible incident.
Sai suka cigaba da zungurarta har sai da ta bada ba’asin wannan mahimmin al’amari.

Her sisters envied her bitterly,
‘yan uwan nata suna mata matsananciyar hassada,

and they were extremely jealous of the boon that was bestowed upon her.
Kuma suna matukar hassadar alherin da ya kwararo mata.

They nagged her all day long until she agreed to call up the Spring of elixir,
Badare ba rana suka takura mata har sai takira Furen fulawar rayuwa (Spring of elixir)

and took him into a dip with her in the swimming pool.
Kuma ta dauke shi tare da ita zuwa wajen iyo a wurin wanka.

Before midnight, the two of them went down to the swimming pool and filled it up with a ground glass,
Kafin shabiyun dare sai su biyun suka gangare zuwa wajen wankan suka cika shi da guntayen kwalba.

The two sisters were hoping that the person of hairs would get so mad with their sister.
‘yan uwan biyu sunyi tunin mutumin ma’abocin gashin nan zai fusata da ‘yar uwar su.

When he would be injured that he would disappear.
Idan yayi rauni ai zai bace,

and the bountiful door would be closed in her face for good.
shikenan kofar garabasa zata kulle mata kenan cikin sauki.

So this is our mother’s gift to her pampered daughter.
Ashe wannan itace kyauta uwarmu ga ‘yar lelen ‘yar tata.

A constant inheritance that never runs out.
Gadon da bazai taba karewa ba.

When the youngest girl burned the second hair,
Lokacin da yarinya ta kona gasin na biyu,

the handsome man appeared again.
Sai kyakkyawan mutumin nan ya sake bayyana.

She kept asking him to swim with her in pool until he consented.
Tacigaba da rokon sa suje wurin wanka suyi wanka har saida ya amince.

The minute he got into the water he started to bleed and screamed in agony.
Da shigar sa cikin ruwan sai jini ya fara zuba har yai ta kuwa cikin bakin ciki.

Oh it hits me from the east.
Wayyo yana tabani daga gabas.

Oh it hits me from the west
Wayyo yana taba ni daga yamma

She burned my heart so bad.
Ta kona min zuciya ba dadi.

And now I cannot rest.
Kuma yanzu banida hutu.

And he flew away looking very sick.
Sai ya tashi sama cikin matsananciyar rashin lafiya.

The girl became very worried about the Sprig of elixir.
Yarinyar ta damu kwarai agameda Sprig.

And she could not understand why the water hurt him so much.
Gashi ta kasa gane dalilin da yasa ya samu rauni a ruwan nan sosai.

She regretted listening to her sisters.
Tayi nadamar sauraren ‘yan uwan ta

 

 

At the night she burned the third hair.
Da dare sai ta kona gashi na uku.

But the Sprig of elixir did not show up.
Amma Sprig bai bayyana ba.

The next three nights she burned more three hairs.
Cikin dare uku dake biye ta kone wasu gasussukan uku.

Still, the Sprig of elixir did not show up.
Ha’ilayau Sprig bai bayyana ba.

Left only with one hair to burn.
Gashi daya ya rage mata ta kona.

The girl decided not to waste it.
Yarinyar ta yanke shawarar bazata batashi ba.

And tormented by the young man’s disappearance.
Taji zafin rashin bayyanar matashin nan.

She took it upon herself to travel around the country looking for him.
Sai ta daukar wa kanta tayi tafiya cikin Kasa don neman sa.

She confided in her nanny saying,
Sai ta tsegumtawa mai kula da ita cewa,

Please Dad do not tell anyone that I am gone.
Don Allah Baba kada ka fadawa kowa cewa natafi.

And if someone wanted to see me.
Idan wani yazo yanason gani na.

Tell them that I am sick.
Ka fada musu cewa banida lafiya.

When food is sent up for me.
Duk lokacin da aka aiko min da abinci.

Take it to the poor.
Sai kaba masu karamin karfi.

Her nanny took mercy on her, and agreed to help her.
Mai kula da ita ya tausaya mata, kuma ya yarda da yataimaka mata.

The girl left her house not even sure about her destination.
Yarinya tabar gidan su batare da sanin inda ta dosa ba.

She just walked and walked.
Sai tayi ta tafiya.

Until she found herself in the middle of the deserted area.
Har dai ta samu kanta a tsakiyar yankin hamada.

With only God on top of the world.
Inda babu kome sai ikon Allah.

When she got tired of walking.
Lokacin da ta gaji da tafiya.

She sat down and rest under a tree.
Ta zauna don ta huta a karkashin itaciya.

After a while she raised up her head.
Jim kadan sai ta daga kanta sama.

At the sound of a pigeon and a dove cooing.
Da taji karan tantabara da kurciya suna kuka.

Suddenly she realized that she could understand their language.
Nan da nan taji ashe tana fahintar harshen su.

For she knew that the pigeon was saying to the dove.
Don taji tantabara tana cewa kurciya.

Don’t you know that her sisters are the ones who ground the glass and filled the pool with it so he could get hurt and they could get rid of him?
Shin bakisan ‘yan uwanta ne suka nike gilas suka cika wurin wanka dashi don yayi rauni kinga sun kore kinan ba?

Poor soul! He intends to get back at her to kill her once he is cured.
Kaico! Yayi niyar komawa wajenta yakashe ta da zarar ya warke.

“The Dove asked” But the poor fellow is really sick. I wonder what can cure him?
“Kurciya tayi tambaya” abin tausayi gaskiya yana jin jiki. Ina mamaki ko me zai iya warkar dashi?

The Pigeon answered.
Sai tantabara ta bada amsa.

The best medicine for him is my blood and yours.
Ingantaccen magani shine jini na da naki.

To mixed together to wash his body.
Ayamutsa su awanke jikin sa.

And your meat and mine.
Sai naman ki da nawa.

Boiled to make broth for him to eat.
A tafasa ayi masa romo ya ci.

And my bones and yours.
Da kuma kasusuwa na da naki.

 

 

 

Ground to sprinkle over his wound.
Adakesu arinka barbadawa akan raunin.

And your feather and mine.
Sai kuma gashin ki da nawa.

To be used as broom to sweep away the blood from his bath.
Ayi amfani dashi kamar tsintsiya wajen share jinin da yayi wanka dashi.

The girl could not believe what she heard,
Da yarinyar bata yarda da abinda taji ba.

And stood up and ran after the birds.
Sai kuma dai ta mike tsaye tabi tsuntsayen nan aguje.

Until she captured and slaughtered them both.
Har sai da ta kamasu ta yankesu baki daya.

She carried the fowl and walked on.
Ta dauki tsuntsayen ta kara gaba.

In the morning she found herself approaching a big city.
Safiya nayi tana isowa wani babban birni.

When she walked the street she heard the people talking about the son of the Sultan.
Lokacin da take yawo akan titi sai taji mutane suna maganar dan Sarkin nan.

Who had been indisposed for some time.
Wanda ya kasance ba aganin sa na wani dan lokaci.

And no Doctor could find him a cure.
Kuma babu likitan da ya iya samar masa magani.

She headed directly to the Sultan’s palace.
Kai tsaye tasa kai zuwa fadar Sarki.

For she knew in her heart that the prince was the person she was seeking.
Saboda taji a zuciyarta cewa mutumin nan shine take nema.

She masqueraded as a Doctor.
Sai ta badda kama kamar likita.

And requested permission to attend the ill prince.
Kuma ta nemi izinin duba Dan sarki da bashida lafiya.

When permission was granted by the Sultan.
Lokacin da Sarki ya bayar da izini.

She approached the sick young man.
Sai ta kusanci yaron marar lafiya.

And she recognised in him the same person her heart yearns.
Ta gane shi ashe shine wanda zuciyarta take raya mata.

She was tormented by his pains.
Ta damu da halin da yake ciki.

And when their eyes met he also said to himself.
Lokacin da suka hada idanu sai yace aran sa.

Those are the eyes of my beloved.
Wadannan ai idanun masoyiya ta ne.

The disguised girl asked the servitors to carry the princeto the bathroom.
Yarinyar da ta badda kama ta umarci ‘yan aikin gidan sukai Dan sarkin bandaki.

Where she washed his injured body with blood of pigeon the dove.
Inda ta wanke masa raunin da jinin tantabara da kurciya.

Which she swept away with their feather.
Wanda ta share masa da gashin su.

She sprinkled their ground bones over his wound.
Ta barbada masa nikakken kasusuwan nasu akan raunin.

And she fed him the broth of their meat.
Ta ciyar dashi roman naman su.

Then she laid him in his bed to rest all night long.
Sa’annan ta kwantar dashi akan gadon sa don ya huta duk tsawon daren.

Early in the morning the young man left his bed safe and sound.
Tunda safe yaron yabar gadon sa lafiya da karfin jiki.

Trilling cries of joy filled the royal palace
Kururuwar murna ta cika fadar.

The Sultan asked to see the brilliant Doctor who cured his son.
Sarki ya nemi ganin hazikin likitan da ya warkar da dan sa.

The Sultan said to the Doctor in disguise.
Sarki yacewa likitan dake cikin badda kama.

We are very thankful for your effort in curing our son.
Muna masu godiya abisa kokarinka na warkar da dan mu.

Our palaces and their contents are in your hands.
Fadojin mu da abinda ke cikin su duk suna hannayen ka.

You name your reward and you will surely get it.
Ka fadi ladar aikin ka kuma tabbas zaka sameta.

Slaves, gold, diamond, horses, and houses?
Bayi ne, gwal ne, zinare ne, dawaki ne ko kuma gidaje?

The Doctor said, God safe your majesty.
Likita yace, Allah Yaja zamanin ka.

But I can not ask for anything as a reward for performing my duty
Bana bukatar kome amatsayin ladan aikin da nayi.

The Sultan insisted on rewarding him
Sarki ya nace sai ya biyashi ladan aikin.

And gave him rosary that he held in his hand.
Sai ya bashi charbin dake rike a hannun sa.

And the ring that he was wearing on his finger.
Da kuma zoben dake sanye a yatsar sa.

Of course the Doctor could not refuse the gift.
Hakika likita ba zai iya kin wannan kyautar ba.

He accepted it graciously and left for his home.
Sai ya amsa cikin farin ciki ya wuce gida.

In her house at night the youngest sister burned the last hair
A gidanta da dare yayi sai ta kone gashin na karshe.

She was very anxious to see the Sprig of elixir once more.
Ta kagara da son ganin Sprig.

He surely appeared this time.
Hakika wannan ya bayyana.

But with his sword in his hand ready to cut her head off.
Amma tare takobi ahannun sa da niyar sare mata kai.

 

 

 

Quickly she uttered his own heartrending words.
Sai nanda nan ta furta masa kalmomin dayake amfani dasu.

Then she held up his father’s rosary and ring to his face.
Sa annan ta daga masa charabin Baban sa da kuma zoben adaidai fuskar sa.

He put down the sword immediately.
Nan danan a saukar da takobin.

And asked for explanation
Ya nemi bayani.

She told him the whole story.
Ta fada masa dukkan labarin.

And explained to him that she herself was deceived by her envious sisters plot.
Tayi masa bayanin cewa ita kanta mahassadan ‘yan uwanta sun yaudare ta ne da makircin su.

The Sprig of elixir believed her.
Sai shi Sprig ya yarda da ita.

The next day he proposed to her and they got married.
Washe gari yayi mata baiko kuma sukayi aure.

The prince took his bride.
Dan sarki ya dauke amaryar sa.

To his own palace away from the envy and jealousy of her sisters.
Zuwa fadar sa daga hassada mahassadan ‘yan uwanta.

They begot boys and girls and lived happily ever after.
Sun kuma samu yara maza da mata. Suka zauna cikin farin cikin matuka.

To wannan shine karshe labarin sai mun hadu awani labarin.

If there is a word which is not been understood from this story, you are free to ask.

Idan akwai wata kalma da ba agane ba daga cikin wannan labari, kunada damar tambaya.

Profound thanks.
Godiya mai tarin yawa.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button