Jarumar Kannywood Maryam Gidado(Maryam Babban Yaro) Tayi Auren Sirri.
Alamun Na Nuni Da Cewar Jaruma Maryam Gidado Da Wasu Suka Fi Sani Da Maryam Babban Yaro Itama Allah Yayi Ta Shige Daga Daka Da Sanyinan Saide Jarumar Tayi Auren Ne Cikin Surru Kamar Yadda Wasu Jaruman Suka Saba Yi A Boye Ba Tare Da An Sani Ba.
Hatta Katin Gayyatar Daurin Auren Da Ta Wallafa A Shafinta Wanda Shi Ne Ya Bayyana Tayi Auren Bata Wallafashi Ba Sai Washe Garin Daurin Auren Tana Yiwa Allah Godiya Inda Jarumai Da Masoyanta Suka Tayata Da Murna Tare Da Fatan Zaman Lafiya.
Auren Yazo Ne Daidai Lokacin Da Jarumar Ke Shan Chaccaka Daga Yan Media Kan Yadda Take Wallafa Wasu Bidiyo Da Wasu Suke Cin Zarafinta Takai Aure Har Ta Tsofa Ko Tana Shaye Shaye Da Sauran Aibatawa Wanda Har Takai Ga Ta Fito Tayi Korafi Cikin Bacin Rai Daga Bisani Ta Fito Ta Bawa Masoyanta Hakuri.
Kamar Yadda Ya Bayyana A Katin Auren Jarumar Ta Auri Wani Ne Mai Suna Alh Abdulmumin Hassan A Ranar 17 Ga Watannan Wadda Aka Daura Auren A Filin J-s Gangare Dake Garin Jos Din Plateau State Da Misalin Karfe 11 Na Safe Da Fatan Allah Basu Zaman Lafiya.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.
Munagodiya dasauraranmu.