.
🏥 Magunguna

Karfin Azzakari kankancewar gaba da saurin kawowa harda wanda za suyi aure

Karfin Azzakari kankancewar gaba da saurin kawowa harda wanda za suyi aure

Karfin Azzakari kankancewar gaba da saurin kawowa harda wanda za suyi aure.

 

 

 

Babban sirrin dake tattare da kanunfari domin karfin jiki dana Azzakari da karin Niima maza da

 

 

 

ZUBEWAR GASHI [HAIR LOSS/ALOPECIA]
🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱🦱

Ina mana barka da azumi, fatan members suna cikin koshin lafiya, wannan tsarabar azumi ce bawai na dawo bane kuci gaba da jina, hakan zai faru amma sai na sami hutu tukun insha Allah in muna raye.

Tsarabar ta yau bayani ne dangane da zubewar gashi wato hair loss a turance, ko kuma Alopecia a yaren likita na nufin wani yanayi da mutum kan tsinci kansa na zubewar ko raguwar adadin gashin kansa akalla kwaya 100 a kullum ahankali ahankali tare da kakkaryewarsa, ko ganin ya taho makale jikin abun tace kai, ko kuma ma mutum ya samu kansa gaba daya babu gashin ko gashin ya zube ya maidashi mai sanko aka. Baya zuwa da wani zazzabi, ciwon kai ko kuraje.

Yanayi ne dakan faru ga maza da mata, manya da yara. ma’ana de ba wanda matsalar ta bari in ana maganar jinsi saide duk da hakan bakowa ke haduwa da matsalar ba sannan akwai wasu abubuwa na daban dake kara kusanta wasu da larurar.

IRE – IREN ZUBEWAR GASHI

1. Akwai xubewar gashi baki daya naka wato (alopecia totalis)

2. Akwai zubewar gashin iya kai wanda yake tsalmi tsalmi kamar makero

3. Akwai zubewar gashin kai hade dana jiki baki daya wato ko ina mutum ya rika ganin ba gashi jikinsa musamman gashin gira, gemu a maza, ko gashin ido (Alopecia universalist)

ME YAKE JAWO HAKAN

Takamai mai ba asan meke jawo hakan ba amma de akwai wasu bubuwa daban daban wadanda sauka hada da;

1. Kwayoyin halitta na gado, wato wasu suna gadar hakan ne daga iyaye ko kakanni sakamakon wani sindarin halitta dasu magabatan suka rasa, irin wannan zubewar gashin muna kiransa da (alopecia areata)

2. Akwai zubewar gashi sakamakon kwayoyin garkuwar jikin mutum dake bashi kariya ta hanyar yaki da kwayoyin cuta ajika wanda akarshe suke komawa su rika cin sinadaran dake samar da gashin bisa kuskuren cewa kwayoyin cutane suka shigo jiki alhalin ba haka abun yake ba. Wato (Auto immune)

3. Sai zubewar gashi sanadiyyar karancin sinadarin rayuwa dake taimakawa fitowar gashi da ake kira (androgen) a turance.

4. Zubewar Gashi sakamakon haduwa da wata larura dake bukatar shan magani akai akai musamman masu ciwon suga, ciwon makoko (thyroid problems), maganin ciwon sanyin kashi wato ciwon guiwoyi hannu da kafa, maganin hawan jini, da ciwon cancer, abune da yake common atsakaninsu.

4. Sai zubewar gashi ko sanko musamman ga maza sakamakon yawaitar sinadarin testestorone ajika.

5. Idan mutum na kar6ar radiation therapy aka, wato amfani da zafi yayin kone wasu kwayoyin cuta ajika akan mutum musammn cutar kansa.

6. Sai canjin sinadaran halitta wanda hakan kan faru ne kurum.yayin da mace ta sami juna biyu cimma shekarun dena haila ko bayan anhaihu.

7. Sai fama da stress wato matsananciyar damuwa afili ko kuma acikin ciki wato physical or emotional stress

8. Yawan canza salon kitse kitse da gyare gyaren gashi.

Wadannan sune mahimman abubuwan da suke jawo zubewar gashi.

WAYE YAKE CIKIN HATSARIN KAMUWA DA HAKAN

1. Mahimmin abunda ke jawo mutumin ya fuskanci zubewar gashi shine Gado (genetic predispositions) idan har acikin dangi ko aka sami mahaifiya kanta ta ta6a ko tayi fama dashi toh kema amatsayin ya’ zaki iya gada. Idan akace gado basai iyaye wanda kasani ba hatta kakarki ta 10 dako a tarihi mamarki ko babanki ma basu san zancenta ba kina iya daukowa daga ita ta hanyar iyayenki walau dangin uwa kona uba. Kuma wannan shike dauke da kaso 85% cikin dari.

Sauran 15% din duk kurum sun taru ne a:

2. Shekaru a wato shekarun tsufa, a lokacin tsufa abune da yake normal ba larura ba dan anga gashi na zubewa, haka kuma a musamman macen data fara manyanta ta cimma shekarun dena haila shekara 40 zuwa 50 aduniya.

3. Kasancewa cikin damuwa koda yaushe (stress)

4. Me fama da ciwon suga

5. Me dauke da ciwon cancer

6. Mutumin da kullum yake kara ramewa haka kurum

7. Karancin ingantaccen abinci ajika wato mutum mai dauke da ciwon yunwa.

MATAKAN KARIYA

Abubuwan da mutum zai taimaki kansa musamman mai larurar ko wanda ma baida ita kuma baya fatan ya kamu sune:

1. Wajibine mai wannan matsalar ya kauracewa shan taba ko inda ake shanta

2. Dena yin kitse kitse masu matukar d’ame kai

3. Tsayar da shan magungunan dake haddasa zubewar gashin, wato in aka ga sakamakon shan maganin wani ciwon gashi na zuba sai asanar wa da likita acanza da wani.

4. Akaucewa bude kai acikin rana wato ya zamto zafin ko hasken rana na dukan kai.

5. Idan kana da ciwon da baya jin magani wato cancer kuma ana maka chemotherapy to karoki likita asamar maka da cooling cap ta sawa aka hakan na taimakawa

TAYA LIKITA ZAI BANBANCE IRIN ZUBEWAR GASHIN DAKE DAMUNA

Eh kamar yadda na fada abaya xubewar gashi iri iri ne, shyasa magani daka bai zama dole yayi ba ko a asibiti sai likita yai binkice awani lokacin ma anbukaci karin gwaje gwaje kafin a gane takamaiman irin matsalar mutum.

Wanda wannan tasa dan mutum yaita yawan zuwa kananun asibitoci da wuya aga sauki, haka ko maganin hausa na gida mutum keyi sai yayi ya gaji domin ba ainishin tushen inda matsalar take aka magance ba. Amma de ahakikanin gaskiya likita baya sa akai ga gwaje gwaje adalilin zubewar gashi domin abune da inkasan aiki daga sign and symptoms da history zaka fahimci inda abun yake.

Amma inta kama dole a asibiti muna yin;

1- BLOOD TEST: Gwajin jini domin kawar da tunanin wasu sauran cuttukan ko fahimtar inda ciwon yake walau kwayoyin garkuwa ne ke cin jiki akaran kansu, ko kuwa kwayoyin halittun gado ne.

2- SCALP BIOPSY: a kokon kan mukan sa abu mudan kankaro sannan mu mika dakin gwaje gwaje aduba wannan specimen da muka kankara domin gano ko kwayar cutace ta sa hakan ko a’a

3- POLL TEST: Likta kan duba layukan gashin ahankali tare da gwado jawosa ko rike tsakiyar gashi da gashi ya fusga dan gwada kwarin gashin.

WANNE IRIN LIKITA YA DACE NA GANI IN NAJE ASIBITI

Wannan matsalace dake cikin dangin larurorin fata, don haka likitan fata shi ake gani wanda muke kiransu da DERMATOLOGIST a yaran likitanci, idan ta kama sai sun nemi dauki toh sukan hada karfi da karfe da masana sinadaran jiki wato ENDOCRINOLOGISTS

A WANNE IRIN ASIBITI AKE SAMUN SU

Tabbas ba kowanne irin asibiti suke ba koda kuwa anga ginin asibiti mai girma ne, saide akan basu lokaci sukan ziyarci irin GENERAL ko COMPREHENSIVE Health center lokaci lokaci.

Amma de ana samunsu a asibitoci irin su Specialist hospital, Medical centers ko Teachings Hospital,.Sai kuma dake irin wadannan likitocin akan samesu da asibitoci na kansu duk inda kaga SKIN CLINIC nan ma ana iya dubaka.

MENENE MAGANIN LARURAR

A hakikanin gaskiya kamar yadda cikakken abunda aka fahimta yana jawo wa shine auto immune babu wani magani daya da za’a ce 100% na maganin matsalar, hasali ma ba wata abar damuwa bace saide dake takan sa damuwa ga wacce abun ya dama musamman a mata. Saide wani lokacin gashin kan toho da kansa batare ma da magani ba.

Amma duk da haka akan basu supportive treatment dakan taimaki gashin ya dena zuba, ya kara masa karfi tare da taimakawa tohowar wani sabo. Saide maganin yakan dau satittuka ko watanni anayi ya danganta da irin tsananin zubewar.

➡ Akwai magunguna na shafawa aka da basa bukatar umarnin likita a rubuce wato (Over the counter Cream) wanda mutum zaije ya saya ya rika shafawa, saide zuwa ga likitan yana da mahimmanci saboda shi zai gane irin munin ciwon da tsarama ko sau nawa zaka shafa da kuma tsawon lokaci.

Daya daga cikin wannan maganin gashi zan fadamuku ganin OTC ne saide duk da haka ya danganta da yanayin karfin zubewar gashin kamar yadda nace dangane da sau nawa ya kamata ai amfani dashi. Maganin shine MINOXIDIL (ROGAINE) 5% ko 15%

Minoxidil shine sunan da likitoci ke amfani dashi arubutunsu, yayin da ROGAINE shine sunan dasu yan kasuwa masu saida magunguna sukafi kira.

YA AKE AMFANI DASHI LIKITA ?

Ana shafawa ne bayan anwanke kai da ruwan dumi ko na sanyi an tsane ruwan toh da ragowar lemar sai a tatso abi kan konkon kan ake shafawa a duk inda babu gashin ahankali ahankali ko asa wani ya taimaka ya shafawa mutum ba duk kan ba saide in rashin gashin gaba daya kanne.

Wanda zubewar gashin yai yawa ake iya gani mukan sasu shafawa sau 1 akullum na tsawon sati 2 sati 4, wata 1 har wata 3 ko 6.

Wasu kan shafa sau 2 asati har wata 6 idan kan ya zube sosai

Wasu kan shafa sau 3 asati na wata guda.

Wannan tasa nace zuwa ga likita ya tsarawa mutum shine.

➡ Haka likitoci kan rubuta magani dangin CORTICOSTEROIDS irinsu; BENZOYL PEROXIDE CREAM wanda shima na shafawa ne wanda shine kusan shine akan zaba a sahun farko wato First Line of Treatment. Shima ana amfani dashi kamar yadda ake dana farko.

Akwai kuma maganin da iya maza ake bawa baya aiki a mata shi na shane (oral) galibi don haka bazan fadesa ba domin yana bukatar sahalewar likita saboda gudun hatsarin dakan biyo magani wato (Adverse Drug Reactions).

Haka kuma akwai wanda ke aiki a mata da maza nasha idan ta kama wanda akan hadashi lokaci guda sanda ake shafa wancan shi kuma ya zamto ana shansa.

➡️Saide nashan wanda zan iya fada muku ku hada wancan na shafawan koma ku saya kuke shan 1 shikadai kullum na tsawon kamar sati 2 ko 3 shine VITAMIN E (TOCOPHEROL) saboda shima bamai hatsari ne ba sai in anwuce ka’ida.

➡️Sai abu na karshe in hakan taki toh saide aima mutum dashen gashi wanda yake da matukar tsada sai anshirya.

Wannan shine bayani dangane da zubewar gashi fatan mun anfana, Allah yasa mu dace

Ibrahim Y. Yusuf
Muna godiya kwarai Allah yajikan magabata

C.E.O_Founder_OF_Educatetimes _Auwal_Telan Gayu

Hello my Fallowers My Name is_Real_Auwal_Telan Gayu_ C.E.O_Founder OF_MR ATG News.com_my followers this is Whatsapp number_ 09133596443_ Only Whatsapp number Don't call me just send me your message Thanks

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button