.
📻 Labaran Hausa

Ban san ina da ciki ba, inji budurwar da ta haihu a jirgin sama

Ban san ina da ciki ba, inji budurwar da ta haihu a jirgin sama

Ban san ina da ciki ba, inji budurwar da ta haihu a jirgin sama

Wata budurwa wacce bata san tana da ciki ba ta haihu jirgi na sararin samaniya. Matar mai suna Tamara ta kwashi hanya ne zata wuce Ecuador daga Madrid, Spain a jirgin KLM Royal Dutch, dimokuraɗiyya ta ruwaito.

An samu bayani kan yadda Tamara kwatsam ta hau jirgi wanda ana gab da isa Netherlands ta fara jin ciwon ciki. Sakamakon jin ciwo, Tamara ta nufi bandaki inda ta nemi yin bayan gida kawai sai haihuwa ta yi.

Kamar yadda Daily Star ta ruwaito, Tamara ta haihu ne bayan yunkurin nakuda biyu.

“Ana saura awoyi kadan kafin su sauka a Netherlands, sai ta fara jin ciwon ciki inda ta nufi bayi. Ga mamakinta, yunkuri biyu kadai tayi ta haihu,” kamar yadda kakakin asibitin Spaarne Gasthuis Haarlem Zuid ta sanar da NL Times.

Matar da dan duk suna lafiya lau kamar yadda likitoci biyu suka bayyana, bayan sun taimaka wa matar ya haihu.

Jaririn wanda aka sanya wa suna Maximiliano ya ci sunan ne bayan wani mutum wanda ya kasance da matar gabadaya lokacin.

Daga saukarsu Netherlands, an wuce da Tamara da jaririnta asibitin Spaarne Gasthuis Haarlem.

Wani labari Yadda Miji yaje ya gawa Mahaifin Uwargida Bata masa Wanka kamar yadda Amarya ke masa

Wani magidanci yana da matarsa da yaransa mata guda hudu ya kara aure, amarya ta zo da sabuwar kissarta, idan gari ya waye sai ta shiga da miji bandaki (irin bandakin nan na tsakar gida) ta yi masa wanka, abun yana damun uwargida, domin idan ana yin wankannan har wake-wake amarya ke yi yaranta suna ji su yi ta dariya ana yiwa baba wanka, don haka da ta ga amarya ta dauko ruwan wanka za ta kora yaranta daki ta kunna rediyo, a haka har aka kwana bakwai.

Sai dai bayan Gogan na ka ya koma hannun uwargida sai ya ce magana ta gaskiya ya saba da wankan amarya don haka dole itama ta dinga yi masa wanka, uwargida ta ce yayi hakuri da wankan yara za ta ji ko da na sa, ya ce shifa dole sai an yi wankannan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button