Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne
Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne

Mai Sayar da Kayan Marmari Yaki Karban Sabon Kudin Da CBN Ya Fito Dashi, Yace Jabu Ne
Wani mai sayar da ‘ya’yan itace ya ki karban sabon takardar kudin Naira da babban bankin Najeriya CBN ya bullo da shi.
A wani faifan bidiyo da Mama ta wallafa a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba, mai sayar da ’ya’yan itacen ya ce bai san sabon kudin Naira ba.
Matakin nasa ya haifar da martani tsakanin masu amfani da TikTok wasu daga cikin wadanda suka goyi bayan mutumin yayin da suka ce har yanzu bayanan ba su yi yaduwa ba.
Masu amfani da TikTok suna maida martani kan wani faifan bidiyon wani mai siyar da kayan marmari da ya ki amincewa da ya karbi sabon kudin Naira na CBN.
An dauki mai siyar da ‘ya’yan itacen a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu sosai a ranar Alhamis, 15 ga Disamba bayan wani mai amfani da TikTok da aka sani da Mama ya wallafashi.
Bidiyon mai tsawon dakika 21 kacal ya isa ya nuna yadda mai sayar da ’ya’yan itace ke shakkar cewa sabbin takardun Naira na sahihai.
Mama na kan hanyar wucewa ta yanke shawarar siyan kayan marmari wanda ta gani ana siyarwa a bakin titi.
Mai sai da kayan marmarin ya hada ya kai mata bakin mota, amma abinda ya faru shine mutumin ya ki karbar kudin da ta bashi.
Daga karshe dai mama ta sanar da shi wannan kudin da yake gani sune sabbin kudin da aka canjawa fasali, amma mutumin yayi biris.
A wani labarin kuma
“Bana neman afuwar ka Kai Ibrahim Sarki Yola, a wajan Allah nake neman Sassauci, Kuma Ina bawa Almajiraina hakuri zanje Lahira a madaukaki “Kalmar Shekh Abduljabar Nasir Kabara ta karshe a kotu
Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba – Sheikh Abduljabbar Kabara
Kai tsaye daga Kotun Ƙofar Kudu.
Kotu ta ce, ta samu Abduljabbar Kabara da laifin yiwa ma’aiki (s a.w) kage da cin mutumcin ma aiki da cewar yayi fyade ,
An same shi da laifi karkashin sashe na 382 (B)
Lauyan da ke kare shi Barrister Aminu Abubakar yace ayi masa sassauci saboda kuskuren fahimta ce tasa Malam Abduljabbar ya aikata wannan laifi.
Amma nan take malamin ya miƙe ya ce shi dai ba da yawunsa ba, Lauyana yake magana.
Malamin ya ce, baya neman sassauci, kuma yana neman a gaggauta yi masa hukunci domin zai yi mutuwa ta girma.
Ku ci gaba da bibiya, zamu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa.