.
🏥 Magunguna

Domin Gamsar

Domin Gamsar

Sirrin Yadda Zaki Karawa Kanki Sha’awa Domin Gamsar Mai Gida Yayin Jima’i A Sauwake.

Ga Duk Wadda Take Son Karawa Kanta Ni’ima Tare Da Gamsar Da Mai Gida Yayin Saduwa To Ka Yadda Zatayi Hadi

Karin Sha’awa.

Wasu matan kan yi kukan rashin sha’awar jima’i. Akan samu mata da ke fama da wannan matsala da har ta kai ta kawo, a dole ta ke saduwa da mijinta, amma ba wai don ta na da sha’awar jima’in ba. Da iznin Alla idan ta yi wannan hadin ta yi amfani da shi za ta kasance mai sha’awar jima’i.

Kayan Hadin Da Ake Bukata:

a.  Sassaken Baure, babban cokali 5

b. Kanumfari, babban cokali 3

c. Zuma, babban cokali 2

d. Lipton

Yadda za ta hada, za ta daka sassaken bauren bayan ta bar shi ya bushe don ta samu garinsa.

Sai ta daka kanumfari, shi ma don ta samu garinsa. Za ta gauraya garin kanumfarinta babban cokali 3 da garin bauren babban cokali 5, bayan ta tabbatar sun gaurayu sai ta zuba zuma babban cokali 2 ta cakuda su, su cakudu sosai.

Za ta debi karamin cokali daya na wannan hadi ta zuba cikin ruwan lipton ta sha sau biyu a rana. Sauran bayani mu na jiran amsar ki a sashen “Comment” na wannan shafi na “Mujalla”.

Gamsar Da Maigida.

Kayan Hadin Da AKe Bukata.

a. Garin gero (Amma kar a surfa)

b. Garin furen(huda) tumfafiya babban cokali 3

c. Garin ‘ya’yan zogale babban cokali 3.

Bayan an samu garin wadannan abubuwa sai a gauraya su, mace ta ke shan karamin cokali sau biyu a rana

Allah Yasa Mu Dace Ameen.

Hanyoyi daban daban da za’a bi domin hada maganin karfin azzakari.

(1) Madara ruwa ko gari.
(2) Man kustulhindi gari.
(3) Citta gari ko ruwan.
(4) Zuma mai kyau.

Yadda za a hada…

A samu Madarar mai kyau yar waje ko peak milk da sauran madara dai mai kyau, za’a tsiyaya ruwan chitta ko garin citta daidai misali.

Sai a samu garin Kustul Hindi cokali daya a zuba aciki, daga nan se a sanya zuma daidai Misali se a shanye hadin duka, Minti 30 kafin kwanciya.

MAGANIN ƘARFIN AZZAKARI DA MAN JIR-JIR

– MAN JIR-JIR
– GARIN JIR-JIR
– GANYEN JIR-JIR.

Duk wanda akayi amfani dashi ya wadatar. Cinsa ko shansa kawaiya wadatar shi Man Jirjeer yana Qone majinar kwankwaso, da majinar ƙirji. Don haka yana ƙara ma Namiji ƙarfi matuka.

Wadanda suke zaune a Qasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa ‘danye cikin sauki. za a saka a abinci ko ama kwada aci.

ƘARFIN AZZAKARI DA MAN HABBATUS SAUDA

A SAMU

-Ganyen na’a na’a danye ko busasshe.
-Man habbatussauda.

Za ayi tafasa ganyen na’a na’a din da dan yawa haka kamar shayi. A zuba mas Man Habbatus Sauda cokali daya sannan asha. Safe da dare kafin kwanciya. in shaa Allah yana bada maana sosai matuka.

ƘARFIN AZZAKARI DA ƘWAN TATTABARA KO ƘWAN KAZA.

A nemi Qwan Tattabara ko ƙwan Kazar gida guda biyu ko uku, a zuba garin habbatus Sauda cokali guda aciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun masu kyau aci.

Allah yasamudace Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button