Ibrahim Birniwa Ya Bayyana Dalilin Na Daina Rubutu Fim Din Labarina.
Ibrahim Birniwa Ya Bayyana Dalilin Na Daina Rubutu Fim Din Labarina.

Ibrahim Birniwa Ya Bayyana Dalilin Na Daina Rubutu Fim Din Labarina.
Shahararren marubucin fina-finan Kannywood Ibrahim Birniwa ya ce ya daina rubuta fitaccen fim din Labarina mai dogon zango saboda rashin jituwa tsakaninsa da masu shirya shi da kuma aiki kan nasa fim din.
Duk da cewa rashin jituwa ce ta sa marubucin ya fita daga fim din, sai dai ya ki fada wa BBC Hausa ainahin abin da ya faru, yana mai cewa da ni nake rubuta fim din da zuwa yanzu ya zo karshe”.
Da yake magana ta cikin shirin Amsoshin Takardunku na Sashen Hausa na BBC a karshen mako, Birniwa ya ce ba zai yiwu ya koma rubuta labarin fim din ba a nan gaba saboda wasu dalilai.
Ga masu bibiyar fim din na Labarina, za su lura da daina ganin sunan lbrahim Birniwa a cikin marubutansa, inda Nasiru Gwangwazo da Yakubu M. Kumo da Saddika Yahaya da Maimuna Beli suka maye gurbin sa.
Birniwa ya ce duk da ba salin-alin suka rabu da mashiryan Labarina ba, wanda Aminu Saira ke ba da umarni, amma dai ba baram-baram suka rabu ba kamar taurarin fim din Nafisa Abdullahi(Sumayya) da Nuhu Abdullahi (Mahmud).
“Kafin fim din Labarina, mun yi ayyuka da dama da Aminu Saira, wasu manyan fina-finai da ya ba da umarninsu, ni ne na rubuta su, saboda haka muna da alakar da ba za a yi baram-baram ba,” in ji shi.
“Abin da ya faru bai kai a kira shi baram-baram ba duk da cewa ba haka aka so ba.
Kamar yadda na fada, akwai ayyukana da na saka a gaba”.
Yanzu haka fim din Labarina da ake haskawa a tashar Saira Movies ta dandalin YouTube da kuma tashar talabijin ta Arewa 24 na zango na biyar bayan fara haska shi a watan Yulin 2020.
brahim Birniwa ne marubucin fim din har zuwa tsakiyar zango na uku, kamar yadda ya fada wa BBC.
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar ya ci gaba da rubuta fim din, ya amsa da cewa:
“Ko da akwai yiwuwar dawowar ma zan ce maka a’a, saboda da ni nake rubuta labarin da na kai shi wajen da ya kamata a ce ya kare Sannan ko su da suke rubutawa ma ina tsammanin sun zo karshe. Watakila sun gama rubuta labarin daga nan har zuwa karshe.”
BBC ta tuntubi Aminu Saira game da zargin amma ya ce “ba na son saka baki a irin wadannan maganganun, ba zan ce komai ba.
Birniwa ya ce aikin da ya sa a gaba shi ne na Matasa Games’ da ake haskawa a gidan talabijin na Arewa 24, wanda ya ce ‘yanzu ma aka fara haska shi”.
Masu sauraranmu a Koda yaushe bayan Kun karanta wannan labarin zamu so karben a sahen mu na tsokaci.