.
📻 Labaran Hausa

Majalissar Dattawa Zatai Muhawara Yau Kan Batun Tsarin Babban Bankin CBN Na Kayyade Cire Kudi

Majalissar Dattawa Zatai Muhawara Yau Kan Batun Tsarin Babban Bankin CBN Na Kayyade Cire Kudi

Majalissar Dattawa Zatai Muhawara Yau Kan Batun Tsarin Babban Bankin CBN Na Kayyade Cire Kudi

A yau majalissar dattijan Nigeria zata kalkale maganar tsarin da babban bankin kasa CBN ya biniro da shi na cire kudi.

Daya daga cikin yan majalissar dattijan ne ya ja hankalin majalissar kan batun inda yace zai takura talakawan kasar nan musamman ma yan kasuwa.

Tun satin da ya gabata majalissar ta sanar da wannan satin a matsayin satin da zatai muhawa kan batun na CBN.

Abuja: A jiya ne majalisar dattijai ta yanke shawarar yin muhawara kan tsarin kayyade kudaden da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi a kwanan baya a zaurenta.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya bayyana haka a zauren majalisar, biyo bayan wani kuduri da sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta Arewa, Olubunmi Adetunmbi ya gabatar.

Sai dai muhawara bata yiwuba, sabida shugaban kwamitin kula da bankuna na zauren majalissar dattijan bai samu damar halartar muhawarar ba, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

 

Sanatan dai ya ja hankalin takwarorin sa kan rashin halartar shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin bankuna da inshora da sauran cibiyoyin kudi Uba Sani daga zauren majalisar.

Misis Ahmad, wacce ita ce mataimakiyar gwamnan babban bankin CBN kan tsarin daidaita harkokin kudi, ta bayyana wa kwamitin cikakkun bayanai game da tsare-tsaren bankin ranar Juma’ar da ta gabata bayan wani mitin da sukai da kwamitin.

An gabatar da cikakken bayanin da babban bankin na CBN ya bayar domin muhawara tare da tantance batun a zaman majalissar na jiya.

Sai dai Adetunmbi ya ce ba za a iya yin muhawarar ba saboda shugaban kwamitin wanda shi ne dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, a jihar Kaduna, ya na jihar sa wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na shiyyar Arewa maso Yamma.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button