.
📻 Labaran Hausa

Kamaye yayi Allah wadai ga masu yada labaran karya akan ‘yan fim tare da bayyana cewa yana nan a raye.

Kamaye yayi Allah wadai ga masu yada labaran karya akan ‘yan fim tare da bayyana cewa yana nan a raye.

Kamaye yayi Allah wadai ga masu yada labaran karya akan ‘yan fim tare da bayyana cewa yana nan a raye.

Kamar yadda kuka sani dai a kwana kin baya kadan da suka gabata ne ake ta cece-kuxe akan wani labarin karya da aka yada shi, kan jarumin wasan kwaiwayo Kamaye na cikin shirin Dadin Kowa.

Labarin ya dauki hankulan jama’a da dama wanda daga baya kuma aka karyata labarin, inda shima kan sa Kamayen ya fito ya bayyana kan sa yana mai karyata labarin yare da sanarwar yana nan a raye.

A yau kuma a wani rahoto da muka samu daga shafin “Fim Magazine” Sun wallafa labarin cewa, Kamaye yayi turda labarin karya akan ‘yan Kannywood, sannan yace yana nan bai mutu ba.

Jarumi kuma babban furodusa Malam Dan’azimi Baba Cediyar ‘Yan Gurasa wanda aka fi sani da Kamaye, ya karyata labarin da ake yadawa cewa wai ya rasu.

Tun a safiyar jiya Laraba dai aka tashi da yaduwar labarin aka shafe tsawon wuni ana baza shi a soshiyal midiya, har ta kai wasu suka dauka gaskiya ne, suna buga fosta da rubutun Allah ya jikan shi.

Amma jarumin na cikin shirin Dadin Kowa ya yi magana da Mujallar Fim kan labarin ya ce:

To ni dai haka na ga labarin a soshiyal midiya kuma daga baya ake ta bugo mini waya ana cewa na mutu.

Ni dai a yanzu ina nan da rai na ban mutu ba, kuma lafiya na ke ina cigaba da harkokin da nake yi.

Jarumin ya yi Allah wadai da masu yada labarin kanzon kurege game da ‘yan fim a soshital midiya.

Ya ce: Ban san abin da ya sa wasu suka mayar da irin wannan labarin na karya a amatsayin labarin da zasu dora a shafin su ba, wai don su na son a rinka bibiyar su.

Wannan ba aikin jarida ba ne, shirme ne kawai da bata sunan mutum da kuma tayar da hankalin jama’a, don a yanzu duk masoya da masu kauna ta da su ka ga wannan labarin hankalinsu ya tashi.

Malam Dan’azimi ya yi kira ga masoyan sa da su kwantar da hankalin su.

Ya ce, Ina kira gamasoya na su kwantar da hankalin su, ina nan da rai na cikin koshin lafiya, ban mutu ba, kuma ina yi wa kowa fatan alheri sabida kaunar da aka nuna mini.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa, ba wannan ba ne karo na farko da aka yada labarin karya game da jaruman Kannywood musamman mutuwa, wannan labarin ya na daga cikin wadanda suka fi daukar hankalin mutane sosai.

Rahoto daga Fim Magazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button