NA ZAUNE BAI GA GARI BA: (NUƘUƊOƊI 10 DAGA HUƊUBAR SALLAR JUMA’AR HARAMIN MAKKAH
Maudu’in Huɗubar Sallar Juma’ar na ranar 18/11/2022 a Haramin Makkah an yi ta ne akan ‘Bushara’ ga muminai. A cikin hudubar, limanin ya yi ƙoƙarin ya karantar da tanadin da Shari’a ta yi ga Musulmai ta fuskar sauƙaƙa mu’amala da zamowa jakadun alheri.
Daga cikin ababen da limanin ya tattauna akwai:
1. Ya bayyana cewa za a iya taƙaita aikin Annabawa da Manzanni cikin kalmomi biyu; Bushara ga waɗanda suka yi imani da Gargaɗi ga waɗanda suka kafirce.
2. Ya kawo bayanin cewa lokacin da Manzon Allah (SAW) ya aiki Mu’azu Ɗan Jabal da Abu Musa Al-ash’ariy (RA) zuwa Yemen ya musu wasiyya da cewa: “Ku sauƙaƙa wa mutane kar ku ƙuntata musu. Ku musu bushara da alheri kar ku kore su daga addini.
3. Limamin ya hakaito cewa da Ibnu Hajrin (Allah ya gafarta masa) ya zo sharhin hadisin sai ya ke cewa: “wannan hadisin yana nuna izuwa ga cewa ya kamata a lallaɓa wanda yake kusa da musulunta don a samu ya musulunta, haka kuma hadisin na nuna cewa tankiya da wa’azi akan saɓon Allah ya kamata ne a yi ta cikin natsuwa da tausasawa. Haka kuma a wajen karantarwa ma ana buƙatar a bi sannu-a-hankali saboda kar a kore sabon-shiga daga koyon ilimi”.
4. Sannan ya ambaci cewa Manzon Allah (SAW) ya taɓa bai wa Abu-Hurairah takalman sa sannan ya ce da shi ka zagaya bayan katangar nan, duk wanda ka gani cikin mutanen da suka shaida cewa Allah daya ne babu abin bauta sai shi, ka yi musu bushara da aljanna
5. Haka kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa: “A yi bushara ga masu takawa zuwa masallaci cikin duhun dare da cewa suna da aljanna”.
6. Wata rana Annabi (SAW) ya ce da Abu Musa Al’ash’ariy shi da jama’arsa (bayan sallar isha’i): “Ku dakata! Ina muku albishir da cewa ba wata al’umma da ke yin Sallah a wannan lokacin in bayan ku” Abu Musa ya ce: sai muka koma gida cikin farin ciki.
7. Ummul-‘Ala’i (RA) ta ce: Na yi rashin lafiya sai Manzon Allah (SAW) ya zo ya duba ni, sai ya ce da ni: “Albishirinki yake Ummul-‘Ala’i! Allah yana kankare zunuban mumini ta hanyar rashin lafiya”
8. Lokacin da aka yi yaƙin (Waƙ’atul Harrah) Anas (RA) ya shiga damuwa sosai saboda ƴan uwa da danginsa da aka kashe a wannan fitina.
Sai Zaid Ɗan Arƙam ya rubuta masa saƙo cewa: “Ina jajanta maka wannan bala’in da ya faru, sannan kuma ina samar da kai cewa na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Ya Allah ka gafarta wa Ansaraw da su da ƴaƴansu da jikokinsu”.
9. Haka ake son mumini ya kasance; mai kyakkyawan tunani da hangen nesa da bin abubuwa sannu-a-hankali da arashi mai kyau da rage wa ɗan uwansa raɗaɗin jarabawa ko fitina in ta same shi.
10. Haka dai ya yi ta kwararo nassoshi ba ji ba gani waɗanda ke nuna irin yadda musulunci ya yi horo da natsuwa da taka-tsantsan da bin abubuwa a sannu da hani game da yarfe ko kaushin hali ko nunkufarci ko murna idan wani ya shiga jarabawa da ire-iren su.
Ni dai haka na yi kasaƙe ina ta jujjuyae maganar a zuciya ta, ina kuma auna ta da halin da muke ciki a farfajiyar kira zuwa ga Addini a ƙasar mu.
Allah Ubangiji ka sa mu dace.