MU TATTAUNA Kamfanin jaridar Dokin Karfe suka wallafa cewa:

Tsakanin kujeran Shugaban Kasa da kujeran Mataimakin Shugaban Kasa wacce kujera ya kamata ‘yan Arewa su hada kai su mara wa baya a zaben 2023?
Ni a fahimtata kujeran Shugaban Kasa ya kamata ‘yan Arewa mu mara wa baya, saboda Shugaban Kasa shi yake da cikakken ikon ya aiwatar da abinda ya ga dama, sabanin kujeran mataimaki wanda bai wuce matsayin ya bada shawara ba, idan aka ga dama a karba ko ayi watsi da ita
Sannan idan muka duba cancanta tsakanin Atiku da Kashim Shettima akwai banbanci, Kashim ya rike kujeran Gwamna inda yake da cikakken iko amma bai iya tsare jiharsa ba, ga zargin cin hanci da rashawa masu tarin yawa a kansa, ya jefa jihar Borno cikin mawuyacin hali
Atiku yayi Mataimakin Shugaban Kasa, duk da bai da cikakken ikon ya sa ayi ko kar ayi amma ya kawo cigaba a yankin Arewa, ya samawa matasa dubbai aiki, kuma ya gina kamfanoni da ake cin moriyarsu a Arewa, sannan ya bada gudunmawa wajen dakile tazarcen Obasanjo
Ba shakka kujeran Shugaban Kasa tafi tasiri, ya zama wajibi mu tashi mu nemota domin cigaban yankin mu
Yaa Allah Ka tabbatar mana da nasaran kujeran Shugaban Kasa a Arewa
MU TATTAUNA
Kamfanin jaridar Dokin Karfe suka wallafa cewa: